'Yan bindiga 7 sun ajiye makamai sun mika wuya da kansu a Zamfara (Hotuna)
- A karkashin shirin samar da zaman lafiya, yan bindiga 7 sun tuba sun mika makamai a Zamfara
- Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ne ya karbi yan bindigar a gidan gwamnati a Gusau
- Sarakuna da wakilai daga hukumomin tsaro suma sun hallarci taron na mika makaman a Gusau
Wasu yan bindiga su bakwai sun rungumi zaman lafiya sun ajiye makamai sun mika wuya a jihar Zammfara.
Gwamnan jihar Bello Matawalle ne ya karbe su a gidan gwamnati da ke Gusau kamar yadda TVC ta ruwaito.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Tubabbin yan bindigan sun mika makamansu da suka hada da bindigu kirar AK 47, alburusai da harsasai fiye da dubu daya.
Wasu daga cikin sarakuna a jihar ta Zamfara sun hallarci taron na mika makaman da rungumar zaman lafiya.
Kazalika, wakilan hukumomin tsaro da suka hada da rundunar sojoji da wasu hukumomin sun hallarci taron.
Asali: Legit.ng