Daga Obasanjo Zuwa Tinubu: Jerin Farashin Canjin Dala Zuwa Naira a Karkashin Shugabannin Najeriya 5

Daga Obasanjo Zuwa Tinubu: Jerin Farashin Canjin Dala Zuwa Naira a Karkashin Shugabannin Najeriya 5

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Dala ta daɗe tana taka rawar gani a kan tattalin arzikin Najeriya a gwamnatoci daban-daban tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a Najeriya.

Ana iya danganta tsadar rayuwa da wahalhalun tattalin arziƙi da ake ciki a ƙasar nan kan tashin da Dala take yi a kullum.

Gggggh
Daga Obasanjo Zuwa Tinubu: Jerin Farashin Canjin Dala Zuwa Naira a Karkashin Shugabannin Najeriya 5
Asali: Facebook

Naira ta ƙara daraja idan aka kwatanta da dalar Amurka a kasuwar canji a ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu, 2024, bayan da ta faɗi ƙasa warwas.

Wasu bayanan ƙididdiga daga kamfanin FMDQ Securities sun nuna cewa a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Najeriya NAFEM, darajar Naira ta kai N1542.5 kan kowace $1 a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rantsar da kwamishinan NPC, ya shiga muhimmin taro da jiga-jigai a Villa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wannan labarin, Legit Hausa ta yi tsokaci kan farashin canjin kuɗaɗe tun daga gwamnatin Olusegun Obasanjo ta shekarar 1999 zuwa kanta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Olusegun Obasanjo – 1999-2023

Gwamnatin Obasanjo ta tarar da farashin canji a hukumance a kan N21.89/$ kuma ta bar shi a kan N128.29/$.

Umar Musa Yar’adua – 2007-2010

A lokacin gwamnatin Yar’adua, farashin canji a hukumance ya tashi daga N128.29/$ zuwa N149.99/$.

Dr Goodluck Jonathan - 2010-2015

An ɗan samu ƙaruwar farashin canji a hukumance a lokacin gwamnatin Jonathan.

Farashin canjin a hukumance ya tashi daga N149.99/$ zuwa N196.95/$.

Muhammadu Buhari - 2015-2023

Dala ta ƙaru a lokacin gwamnatin Buhari, inda ta samu ƙarin sama da kaso 100%.

Farashin canjin a hukumance ya tashi daga N196.95/$ zuwa N461.06/$.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya

Bola Ahmed Tinubu – 2023

Farashin canjin daga babban bankin Najeriya (CBN) ya zuwa ranar Alhamis 22 ga watan Fabrairu, 2024, yana a N1488.396/$.

Darajar Naira Ta Ƙaru Kan Dalar Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa darajar Naira ta farfaɗo a kasuwar ƴan canji bayan ta yi ƙasa warwas a cikin mako guda.

A rana ɗaya darajar Naira ta ƙaru da N100 idan aka kwatatanta da farashin Dalar Amurka inda ta tashi da fiye da kaso 6%.

Asali: Legit.ng

Online view pixel