Yan Kasuwar Canji a Abuja Sun Rufe Shaguna, an Gano Dalili

Yan Kasuwar Canji a Abuja Sun Rufe Shaguna, an Gano Dalili

  • A ranar Alhamis, 1 ga watan Fabreru, 'yan kasuwar canjin kudi a Abuja suka yanke shawarar rufe shagunan su
  • An ruwaito cewa karancin takardun kudi da kuma dawowar hada-hadar kasuwancin 'crypto' ne ya sa rufe shagunan
  • Shugaban kungiyar 'yan kasuwan na Abuja, Mallam Abdullahi ya ce za su zura idanuwa suga abin da Allah zai yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da bakwai a aikin jarida.

Abuja - 'Yan kasuwar canji (BDC) sun sanar da dakatar da aiki a Abuja sakamakon rashin samun wadatattun takardun dalar Amurka.

Shugaban kungiyar 'yan kasuwar, Mallam Abdulahi Dauran ne ya sanar da hakan a babban birnin kasar a ranar Laraba.

Yan kasuwar canji a Abuja sun rufe shaguna
‘Yan kasuwar canji a Abuja sun rufe shaguna, an gano dalili. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ranar da kowa zai rufe shagonsa

Ya alakanta karancin takardun dala da tabarbarewar kasuwancinsu akan yadda kasuwancin dala ya koma a yanar gizo, watau 'crypto'.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike: Ana kukan tsadar rayuwa, Minista yayi karin kudin makarantu a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daurau ya ce rufe kasuwancin zai fara aiki daga ranar Alhamis 1 ga Fabrairu, 2024, Daily Trust ta ruwaito.

Wasu da jaridar The Nation ta zanta da su sun ce sun samu umarni ne daga kungiyar ‘yan canji ta Najeriya (ABCON) na da aina sayar da dalar.

Sai dai wani binciken da aka yi ya nuna cewa sun rufe shagunan ne sakamakon raguwar tazarar da ke tsakanin farashin canji na hukuma da na 'yan kasuwar.

Dalilin da ya sa majalisa ta gayyaci gwamnan CBN

Wannan na zuwa ne sa’o’i bayan majalisar dattawa ta gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, kan rikicin saye da sayar da dala.

Kwamitin majalisar kan harkokin banki, inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi ne ya gayyaci gwamnan CBN.

Gwamnan zai yi bayani bayani kan abubuwan da ake yi na magance matsalar tattalin arziki da hawa da saukar darajar naira.

Kara karanta wannan

APC: Fastocin Yahaya Bello na neman kujerar Ganduje sun mamaye Abuja

Matashi ya angwance da 'yan mata uku a lokaci daya

A wani labarin kuma, wani matashi ya angwance da kyawawan 'yan matansa uku a rana daya, bikin da ya gudana a jiya Laraba.

An ruwaito cewa, matashin mai suna Tersugh Aondona ya angwance da Blessing, Nancy da kuma Sulumshima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel