Kano: Ana Tsaka da Shari'ar Murja, Kotu Ta Ba da Umarnin Kamo Wani Fitaccen Mawaki, Ta Fadi Dalili

Kano: Ana Tsaka da Shari'ar Murja, Kotu Ta Ba da Umarnin Kamo Wani Fitaccen Mawaki, Ta Fadi Dalili

  • Yayin da ake ci gaba da shari'ar Murja Kunya, kotun ta umarci kamo matashin mawaki a jihar Kano
  • Kotun ta umarci kamo Ado Isa Gwanja ne bayan Majalisar Malaman jihar ta maka mawakin a kotu da wasu
  • Har ila yau, kotun ta dakatar da Gwanja daga yin wake-wake har sai an kammala binciken da ake yi a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta umarci 'yan sanda su kamo shahararren mawaki Ado Gwanja.

Kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a, Aisha Mahmud ta ba da umarnin ne yayin da ake zargin mawakin da wasu waken banza.

Kara karanta wannan

Lauyoyin Murja Kunya na shirin daukar mataki 1 tak kan gwamnatin Kano

Kotu ta umarci kamo fitaccen mawaki a Kano
Kotu ta umarci kamo mawaki Ado Gwanja kan wasu zarge-zarge. Hoto: Ado Isa Gwanja.
Asali: Facebook

Wane mataki kotun ta dauka kan Gwanja?

Wannan mataki na kotu ya tabbatar da umarnin Kotun Shari'ar Musulunci a Bichi da ta umarci kama mawakin a bara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta kuma haramta wa mawakin yin waka har zuwa lokacin da rundunar ’yan sanda za ta kammala binciken da ake yi a kan mawakin.

Umarnin kotun na zuwa ne bayan Majalisar Malaman Jihar Kano ta maka Ado Gwanja da wasu a gaban kotu.

Yadda Gwanja ya daukaka kara kan zargin

Majalisar ta na zargin mawakin da amfani da kalaman batsa da ba su dace ba a wakokinsa, cewar Aminiya.

Idan ba a manta ba a shekarar 2023, kotu ta gayyaci Ado Isa Gwanja da Idris mai wushirya da Murja Ibrahim Kunya da 442 da sauransu.

Wau mazauna Kano ne suka maka su a kotu kan zargin bata tarbiyyar al'umma da saba al'adu da koyarwar Musulunci.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun cafke wasu dattawa 2 da kokarin sace kanin gwamnan PDP, sun shiga ha'ula'i tun yanzu

Daga bisani Ado Gwanja da wasu sun garzaya babbar kotun don dakatar da umarnin kotun da ta ce a kama su, cewar BNN Breaking.

Kotun ta ba da umarnin dakatar da 'yan sanda daga kama Gwanja har zuwa lokacin da kammala duba korafinsa na hakkin dan Adam.

Kotu ta ba da umarni kan Murja

Kun ji cewa wata kotu a jihar Kano ta bai wa likitoci umarnin duba lafiyar kwakwalwar Murja Ibrahim Kunya.

Wannan na zuwa ne bayan an gurfanar da matashiyar kan zargin yada badala da karuwanci a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel