An kada gangar siyasar 2019 a Katsina

An kada gangar siyasar 2019 a Katsina

Wasu manyan kusoshi na jam'iyyar APC dake shiyar Katsina ta Kudu sun goyi bayan Abu Ibrahim da a tsaida ahugaban kwamitin hukumar 'Yansanda na zauren majalissar dattawa Sanata Abu Ibrahim takara a 2019.

An kada gangar siyasar 2019 a Katsina
An kada gangar siyasar 2019 a Katsina

Jiga-jigan sun cimma yarjejeniyar sake tsaida Abu Ibrahim takarar Sanata a shiyar da yake wakilta ta Katsina ta Kudu, a wani zama da suka yi a Abuja.

A zaman bayyana amincewar sake tsayawa takarar da jam'iyyar APC ta yi masa, ya same halartar Shugaban walwala da jin dadi, na shugaban jam'iyyar na kasa Alhaji Ibrahim Masari, wanda kuma mataimakin Shugaban jam'iyyar na shiyar Funtua Bala Abu ya bayyana sanarwar.

Bala ya bayyana cewa ya zame masu wajibi da su fitar da Abu Ibrahim saboda namijin kokarinsa a gare mu da daukacin dukkanin al'ummar shiyar Funtuwa baki daya.

Ku biyo mu a Fezbuk: https://web.facebook.com/naijcomhausa/?_rdr

Ku biyo mu a tuwita: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel