Jerin Jiga-Jigan APC da Wasu da Su Ka Caccaki Buhari Kan Jinginar da Rubabbiyar Gwamnati ga Tinubu

Jerin Jiga-Jigan APC da Wasu da Su Ka Caccaki Buhari Kan Jinginar da Rubabbiyar Gwamnati ga Tinubu

FCT, Abuja – Gwamna Dapo Abiodun na daga cikin gwamnonin da su ka yi korafi kan mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a kwanan nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gwamna Abiodun ya ce Tinubu ya gaji lalatacciyar gwamnati da ta kare ba tare da komai da ya rage a gwamnatin ba.

Jerin wadanda su ka kushe tsarin tattalin arziki na gwamnatin Buhari
Jiga-Jigan APC da Su Ka Caccaki Buhari Kan Durkusar da Tattalin Arziki. Hoto: C. Soludo, D. Abiodun, A. Oshiomole.
Asali: Twitter

Wadanda su ka kushe tsarin na Buhari mafi yawanci sun yi martani ne kan yadda Buhari ya nakasa tattalin arzikin kasar kafin barin mulki.

Legit ta yi bincike inda ta jero wasu daga cikin jiga-jigan APC da su ka caccaki Buhari bayan ya bar mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Wani Gwamnan ya sake fallasa yadda aka kai Najeriya gargara kafin zuwan Tinubu

1. Nuhu Ribadu

A farkon watan Nuwamba, Ribadu ya bayyana cewa Tinubu ya gaji asusun gwamnati ba tare da ko sisi ba.

Ribadu, wanda shi ne hadimin Tinubu a bangaren tsaro ya ce rashin kudin da su ka gada shi ya kawo matsala a bangaren kasafin kudin kasar.

Ya ce kudaden shiga da gwamnatin Tinubu da su aka yi amfani wurin cike gurbin abin da aka rasa.

2. Adams Oshiomole

A watan Agusta, Adams wanda Sanata ne a majalisa ya ce Tinubu ya gaji mafi munin tattalin arziki a kasar.

Sanata Adams ya ce matakan da Shugaba Tinubu ke dauka wani shiri ne na farfado da tattalin arzikin kasar.

Oshiomole wanda tsohon shugaban APC ne ya roki ‘yan Najeriya da su kara hakuri da Tinubu za su more a gaba.

3. Dapo Abiodun

Gwamna Abiodun ya ce Tinubu ya gaji lalatacciyar gwamnati musamman a bangaren tattalin arziki ba tare da komai ba da ya rage a gwamnatin.

Kara karanta wannan

Sheikh Bala Lau ya yabawa Uba Sani kan 'inganta walwalar' mazauna Kaduna

Abiodun ya roki ‘yan Najeriya da su kara hakuri inda ya ce matakan da Tinubu ke dauka su ne kadai za su farfado da kasar.

4. Charles Soludo

Gwamna Soludo a ranar 23 ga watan Nuwamba ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya gaji matacciyar gwamnati a bangaren tattali arziki.

Gwamnan Anambra ya ce mutane har yanzu ba su gane cewa tattalin arzikin kasar a mace ya ke ba.

Farfesan ya ce ya kamata zuwa yanzu ace ‘yan Najeriya sun fahimci yadda tattalin arzikin kasar ya gama lalacewa.

Gwamna ya soki tsarin mulkin Buhari

A wani labarin, Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya sake tabbatar da abin da wasu ‘yan siyasa ke fada kan Buhari.

Abiodun ya ce Tinubu ya gaji mafi munin tattalin arziki daga gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel