Kano, Kaduna da Wasu Jihohi 8 a Najeriya da Aka Fi Amfani da Intanet Inji Wani Bincike

Kano, Kaduna da Wasu Jihohi 8 a Najeriya da Aka Fi Amfani da Intanet Inji Wani Bincike

Yanayin amfani da kafafen yanar gizo a Najeriya ya sami ci gaba sosai a cikin shekaru, tare da karin 'yan ƙasar da ke samun damar hawa intanet.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Wannan ya samu ne ta hanyar ingantattun hanyoyin sadarwa, na'urorin hannu masu araha musamman wayoyi da karuwar wayar da kan jama'a kan fa’idar yanar gizo.

Ya zuwa kwata na hudu na 2023, bayanai kan yadda ake amfani da intanet a fadin kasar sun bayyana jihohin da ke kan gaba wajen amfani da yanar gizo.

Alkaluman da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar sun nuna cewa, jama’ar da ke amfani da intanet sun kai miliyan 163.8 ya zuwa karshen shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar EFCC sun cafke ɗaliban jami'ar Arewa, sun aikata wani babban laifi

Jihohin da aka fi amfani da intanet a Najeriya
Jerin jihohin Najeriya da aka fi amfani da intanet a 2023 | Hoto: GettyImages, nigerianstat.gov.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bisa la’akari da bayanan NBS, ga jerin jihohi 10 da suka fi yawan masu amfani da intanet a Najeriya a kwatan karshe na 2023:

1. Legas (miliyan 18.9)

A saman jerin dai jihar Legas ce, cibiyar kasuwanci ta Najeriya da ke alfahari da masu amfani da intanet miliyan 18.9.

Ci gaban abubuwan more rayuwa na jihar, hade da matsayinta na kasuwanci da ci gaban fasaha na daga dalili karuwar masu amfani da intanet.

2. Ogun (miliyan 9.5)

Mai biye da jihar Legas, jihar Ogun da ke makwantaba da Legas din na da akalla masu amfani da intanet sama da miliyan 9.5.

Wannan ya faru ne sakamakon karin ci gaba a fannin ababen more rayuwa da kuma ci gaban fasahar zamani da ake samu a jihar.

3. Kano (miliyan 9)

Jihar Kano a Arewacin maso Yammacin Najeriya ce ta uku a jerin jihohin da aka fi amfani da yanar gizo a Najeriya.

Kara karanta wannan

Sabuwar annoba ta kashe ma’aikatan lafiya uku da marar lafiya a asibitin sojin Najeriya

Jihar Kano na da tarihin kasuwanci da kuma samun ci gaba a duniyar fasaha cikin kankanin lokaci, musamman duba da sauran jihohin Arewa.

4. Oyo (miliyan 8.4)

Jihar Oyo sananniyar jiha ce wajen kayayyakin al’adu masu daukar hankali, wacce a yanzu ke da masu amfani da intanet sama da miliyan 8.4.

Birnin Ibadan na jihar ne babban birnin da ke haskawa a fannin fasaha, ilimin zamani da kuma kirkire a fannin fasahar zamani.

5. Kaduna (miliyan 7.4)

Jihar Kaduna a Arewa maso Yammacin Najeriya na ci gaba da samun karuwar masu afami da intanet, inda a yanzu take da sama da mutum miliyan 7.4.

Kaduna dai ta jima da yin na’am da kayayyakin fasaha, musamman a wannan zamani da matasa ke kara shiga harkar a Najeriya.

6. FCT (miliyan 5.8)

Babban birnin tarayya Abuja na da akalla mutum miliyan 5.8 da ke amfani da yanar gizo, kamar yadda NBS ta bayyana.

Kara karanta wannan

Sanata Sani ya fadi mafita 1 da Musulmi da Kiristoci zasu runguma domin farfado da naira

Hakan ba zai rasa nasaba da yadda shugabannin siyasar kasar ke amfani da yanar gizo ba da kuma samuwar kamfanonin fasaha da dama a birnin.

7. Rivers (miliyan 5.6)

Jihar Rivers na daga jihohin da ke buga kasuwanci a Najeriya, musamman a birnin Fatakwal mai arzikin man fetur.

Jihar na da akalla masu amfani da yanar gizo miliyan 5.6, wanda hakan ke da nasaba da karuwar karbar fasahar zamani a jihar.

8. Adamawa (miliyan 5.4)

Jihar Adamawa a Arewa Maso Gabas na daga jihohin da suka fi ko’ina amfani da yanar gizo a kwatan karshe na 2023.

An ruwaito a rahoton NBS cewa, Adamawa na da mutanen da ke amfani da intanet sama da mutum miliyan 5.4.

9. Katsina (miliyan 4.6)

Jihar Katsina a Arewa maso Yamma na daga jihohin da ke da masu amfani da intanet da yawa, musamman a yankunan birni.

Wannan ba zai rasa nasaba da kari da ake samu a karbuwar amfani da yanar gizo ba jihar mai fama da hare-haren ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bankado hanyoyi 32 na safarar abinci daga Najeriya zuwa kasashen waje

10. Delta (miliyan 4.4)

A karshe, jihar Delta ce ta 10 a jihohin da ke masu amfani da intanet mafi yawa a Najeriya a rahoton NBS.

Jihar mai arzikin man fetur ta samu wannan karin masu amfani da intanet ne duba da yadda fasaha ke ci gaba da zama ruwan dare a kasar.

Jihohin da suka fi girman kasa a Najeriya

A wani labarin, mun kawo muku jerin jihohin da suka fi girman kasa a Najeriya, farawa daga jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya.

A rahoton, mun kawo muku jihar Borno a matsayin ta biyu sai kuma sauran jihohin da suka biyu bayansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.