Jami’an Hukumar EFCC Sun Cafke Ɗaliban Jami’ar Arewa, Sun Aikata Wani Babban Laifi

Jami’an Hukumar EFCC Sun Cafke Ɗaliban Jami’ar Arewa, Sun Aikata Wani Babban Laifi

  • Hukumar EFCC ta sanar da cewa ta cafke wasu dalibai 48 na jami'ar jihar Kwara (KWASU) tare da wasu mutum biyu a ranar Alhamis
  • Kakakin hukumar, Dele Oyewale ya fitar da sanarwar wadda ta yi nuni da cewa an kama daliban ne bisa laifin zamba ta 'intanet'
  • Oyewale bayan lissafa jerin daliban da aka kama ya ce an kwace manyan motoci guda tara, kwanfutoci guda 24 da wayoyi masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kwara - Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) a shiyyar Ilorin sun kama dalibai 48 na jami’ar jihar Kwara.

Jami'an sun kuma kama wasu mazauna garin Malete da ke karamar hukumar Moro a kan wasu laifukan da suka shafi zamba ta Intanet da aka fi sani da “yahoo-yahoo.”

Kara karanta wannan

Jami’an EFCC sun kai samame wurin ‘yan canji a Kano, Abuja da Oyo akan wani dalili 1 tak

EFCC ta cafke ɗalibai 48 na jami'ar Kwara
Daliban jami'ar na zambar kudin mutane ta 'intanet' a dakunan makarantar. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Yadda jam'ian hukumar suka kama daliban

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban sashen yada labarai na EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Ilorin a ranar Alhamis kuma aka wallafa ta a shafin hukumar na X.

Oyewale, ya bayyana cewa kama daliban ya biyo bayan sahihan bayanan sirri ne kan yadda aikin “yahoo-yahoo” ke ta karuwa a jihar, musamman a cikin jami’o’in.

Ya ce jami’an EFCC bayan bincike sun kama wadanda ake zargin a maboyarsu daban-daban bayan kwashe kwanaki suna sa ido a ranar Laraba 21 ga Fabrairu, 2024.

Jerin farko na sunayen daliban da aka kama

Daliban da aka kama su ne Idris Yekini, Ayantola Segun, Adeshina Taheeb, Mustapha Alamin, Usman Harun, Oladimeji Oseni, Qudus Temitope da Adewunmi Israel.

Akwai kuma, Lukman Uthman, Alamin Ibitoye, Usman Sadiq, Musbau Waris, Ibrahim Oluwatosin, Oladele Israel da Rafiu Ashimu.

Kara karanta wannan

EFCC ta tsare tsohon gwamnan Arewa tsawon kwanaki 2 kan wawushe N10bn, ta ɗauki mataki 1

An kuma kama Aransiola Oluwaseun, Akolade Adetola Toheeb, Joseph Samuel, Adewuyi Quadri, Adebayo Olamilekan, Ogunrinde Gabriel da Abolaji Ismail.

Karin sunayen sauran daliban da aka kama

Sauran sun hada da Ogundele Samuel Ejiro, Musa Ali Olawale, Isah Oluwatumishe, Abdullahi Abdulmajib, Abdulralman Abubakar, Olaosebikan Martins da Mazeed Ayomide.

Hakazalika hukumar ta kama Oyeniyi Michael, Moses Bright, Oladipo Victor, Shehu Abdugafar, Abdulmalik Khalid Timileyin, Muhammad Nabil, Adebayo Qudus da Owoeye Adeyanju.

Sauran sun hada da Abdulwaheed Zakariyah, Olaleye Gbenga, Victor Kayode, Samad Olarewaju, Raheem Ayomide, Ismail Abdulbasit, Oluyedun Khalid da Moshood Lawal.

Za a gurfanar da daliban gaban kotu - Oyewale

Jerin sunayen ya ƙare da Utman Abayomi da Aransiola Joshua, yayin da mutum biyu mazauna Malete su ne Babalola Razaq da Godwin Ouna Ejika.

Oyewale ya bayyana cewa kayayyakin da aka kwato daga hannun daliban sun hada da wasu manyan motoci guda tara, da kwamfutoci 24, da kuma nau’ikan wayoyi daban-daban.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ta mamaye titunan Legas, bidiyon barnar da ruwan ya yi ya ja hankali

“Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken da ake yi.”

A cewar Oyewale.

Zanga-zanga: Kungiyoyin kwadago ta yi wa DSS martani

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa kungiyoyin kwadagon Najeriya da suka hada da NLC da TUC sun ce babu wanda ya isa ya hana su yin zanga-zaga a fadin kasar.

Wannan martani ne ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) wadda ta gargadi kungiyoyin kwadagon da cewar za a tayar da tarzoma idan suka yi zanga-zangar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel