Jerin Jihohin Najeriya 10 da Aka Fi Samun Kayan Abinci da Tsada, Kogi Na Kan Gaba

Jerin Jihohin Najeriya 10 da Aka Fi Samun Kayan Abinci da Tsada, Kogi Na Kan Gaba

  • Kogi da Kwara sun sake shiga jerin jahohin Najeriya da aka fi samun tsadar kayan abinci a wannan lokacin
  • Sabbin bayanai sun nuna cewa farashin kayan abinci ya karu sosai da kashi 35.41% a ma’aunin shekara
  • Wadannan alkaluma sun nuna irin gwagwarmayar da ‘yan Najeriya ke yi na ciyarwa da rayuwa a kowane wata

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci a watan Janairun 2024 ya kai 35.41% bisa dari a ma’aunin shekara.

Wannan dai shi ne maki 11.10% mafi girma idan aka kwatanta da hauhawar farashin abinci zuwa 24.32% da aka gani a Janairun 2023.

Kara karanta wannan

An cafke mutane 5 da ‘sace’ buhuna 1800 na abincin ‘yan gudun hijira a Kano

Jihohin da aka fi tsadar kayan abinci a Najeriya
Kogi da sauran jihohi 9 da aka fi tsadar abinci a Najeriya | Hoto: NBS
Asali: Facebook

Hukumar ta kididdigar ta bayyana hakan ne a cikin rahoton farashin kayan masarufi da fitar na Janairun 2024 da ta buga akan shafin yanar gizonta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka samu karin farashin kayayyaki

Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin biredi da hatsi, dankali, doya da sauran sauwowi, mai da kitse, kifi, nama, 'ya'yan itace, kofi, ganyen shayi, da koko su suka haifar da hauhawar farashin kayan abinci.

Wani bangare na rahoton, NBS ta ce:

“An samu hauhawar farashin abinci a ma’aunin shekara sakamakon hauhawar farashin biredi da hatsi, dankali, doya da sauran saiwowi, mai da kitse, kifi, nama, ‘ya’yan itace, kofi, ganyen shayi, da koko.
“A ma’aunin wata, hauhawar farashin abinci a watan Janairun 2024 ya kai 3.21%, wanda ya karu da kashi 0.49% idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Disamban 2023 (2.72%).

Kara karanta wannan

Ku bamu kwana 30, Masu sarrafa siminti sun gindaya sharuda ga Tinubu kan farashin, sun kawo mafita

“Hauhawar farashin kayan abinci a ma’aunin wata ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin dankalin turawa, doya da sauran saiwowi, burodi da hatsi, kifi, nama, taba, da kayan lambu."

Jihohi 10 da aka fi tsadar kayan abinci a Najeriya

  1. Kogi - 44.18%
  2. Kwara - 40.87%
  3. Ekiti - 39.63%
  4. Ondo - 39.59%
  5. Akwa Ibom - 39.96%
  6. Imo - 39.92%
  7. Osun - 39.72%
  8. Ebonyi - 39.14%
  9. Abia - 39.58%
  10. Delta - 38.94%

Jihohin da aka fi tsadar gas din girki a Najeriya

A wani rahoton, NBS ta fitar da jerin jihohin da aka fi samun tsadar gas din girki a Najeriya, inda da aka bayyana su dalla-dalla.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kuka kan yadda kayayyaki suka yi tsada, musamman bayan janye tallafin man fetur.

Sai dai, duk da haka, gwamnati na ci gaba da cewa tana kokarin tabbatar da an samu sauki wajen inganta rayuwar ‘yan kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel