Jerin Jihohin Najeriya 13 Wadanda Suka Fi Fadin Kasa

Jerin Jihohin Najeriya 13 Wadanda Suka Fi Fadin Kasa

Najeriya tana da jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja. Waɗannan jihohin suna da ƙananan hukumomi 774.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wata sabuwar ƙididdigar da shafin @StatiSense ya wallafa a X, ta nuna cewa a cikin jihohi 36 da ake da su a Najeriya akwai waɗanda suke da faɗin ƙasa sosai fiye da sauran.

Jihohin da suka fi fadin kasa
Jerin jihohin da suka fi fadin kasa a Najeriya Hoto: @govkaduna
Asali: Instagram

Ga jerin guda 13 waɗanda suka fi faɗin ƙasa:

1. Jihar Neja

Jihar Neja ita ce jihar da ta fi kowacce jiha faɗin ƙasa a Najeriya. Jihar tana da faɗin ƙasa wanda ya kai murabba'in kilomita 76,383.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihar tana da ƙananan hukumomi guda 21 kuma ta yi iyaka da jihohin Kaduna, Kebbi, Kwara da birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana dalilin da ya sanya ake kashe-kashe a Plateau

2. Jihar Borno

Jihar Borno tana a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya, inda take da faɗin ƙasa wanda ya kai murabba'in kilomita 70,898.

Jihar wacce ita ce ta biyu mafi girman faɗin ƙasa a Najeriya ta yi iyaka da jihohin Yobe, Adamawa da Gombe.

3. Jihar Taraba

Jihar Taraba ita ce jiha ta uku mafi girman faɗin ƙasa a Najeriya. Jihar tana da faɗin ƙasa wanda ya kai murabba'in kilomita 54,473.

Jihar wacce take a yankin Arewa maso Gabas ta yi iyaka da jihohin Benue, Plateau, Adamawa, Gombe da Nasarawa.

4. Jihar Kaduna

Jihar Kaduna tana a yankin Arewa maso Yamma sannan tana da faɗin ƙasa wanda ya kai murabba'in kilomita 46,053.

Jihar ta yi iyaka da jihohin Katsina, Neja, Zamfara, Bauchi, Nasarawa, Kano da birnin tarayya Abuja.

5. Jihar Bauchi

Jihar Bauchi ita ce jiha ta biyar mafi girman faɗin ƙasa a Najeriya. Jihar tana da faɗin ƙasa wanda ya kai murabba'in kilomita 45,837.

Kara karanta wannan

Jega ya bayyana abu 1 da ya kamata a bincika kan zaben 2023

Jihar Bauchi ta yi iyaka da jihohin Gombe, Plateau, Gombe, Jigawa, Kano, Yobe da Taraba.

6. Jihar Yobe

Jihar Yobe na daga cikin jihohin da suke da yawan faɗin ƙasa a Najeriya. Jihar wacce take a yankin Arewa maso Gabas tana da faɗin ƙasa wanda ya kai murabba'in kilomita 45,502.

Jihar Yobe ta yi iyaka da jihohin Borno, Gombe, Jigawa da Bauchi.

7. Jihar Zamfara

Jihar Zamfara tana da faɗin ƙasa wanda ya kai murabba'in kilomita 39,762. Jihar ita ce ta bakwai a cikin jerin jihohin da suka fi faɗin ƙasa a Najeriya.

Jihar Zamfara tana da iyaka da jihohin Katsina, Sokoto, Kaduna, Kebbi da Neja.

8. Jihar Adamawa

Jihar Adamawa ita ce ta takwas a cikin jerin jihohin da suka fi yawan faɗin ƙasa a Najeriya.

Jihar wacce ta yi iyaka da jihohin Borno, Gombe da Taraba tana da faɗin ƙasa wanda ya kai murabba'in kilomita 36,917.

Kara karanta wannan

Filato: Asirin wasu mutane da ake zargi da hannu a kashe bayin Allah sama da 100 ya tonu a Arewa

9. Jihar Kwara

Jihar Kwara tana da faɗin ƙasa wanda ya kai yawan murabba'in kilomita 36,825.

Jihar Kwara wacce ke a yankin Arewa ta Tsakiya ta yi iyaka da jihohin Neja, Oyo, Ekiti, Osun da Kogi.

10. Jihar Kebbi

Jihar Kebbi wacce ke a yankin Arewa ta Yamma tana da faɗin ƙasa wanda ya kai murabba'in kilomita 36,800.

Jihar Kebbi ta yi iyaka da jihohin Zamfara, Sokoto da Neja.

11. Jihar Benue

Jihar Benue ita ce ta 11 a cikin jerin jihohin da suka fi faɗin ƙasa a Najeriya, inda take da yawan faɗin ƙasa wanda ya kai murabba'in 34,059.

Jihar Benue wacce ke a yankin Arewa ta Tsakiya, ta yi iyaka da jihohin, Nasarawa, Kogi, Taraba, Enugu, Ebonyi da Cross Rivers.

12 Jihar Plateau

Jihar Plateau wacce ke a yankin Arewa ta Tsakiya tana da faɗin ƙasa wanda ya kai murabba'in kilomita 30,913.

Jihar ta yi iyaka da jihohin Kaduna, Bauchi, Nasarawa da Taraba.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah na neman Murja Kunya, Gfresh da wasu yan TikTok 4 a Kano, ta fadi dalili

13. Jihar Kogi

Jihar Kogi ita ce jiha ta 13 a cikin jerin jihohin da suke da yawan faɗin ƙasa a Najeriya, inda take da faɗin ƙasa da ya kai murabba'in kilomita 29,833.

Jihar Kogi ta yi iyaka da jihohin Kwara, Nasarawa, Benue, Ekiti, Edo, Anambra da Ondo.

Jihohin da Suka Fi Tsadar Rayuwa a Najeriya

A baya mun kawo muku jerin jihohin da suka fi tsadar rayuwa a Najeriya a shekarar 2023.

Jihohin dai sun shiga cikin wannan jerin a wata ƙiddiga da hukumar ƙididdiga ra ƙasa (NBS) ta fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel