“Tsoho Ya Dawo”: Karamin Yaro Ya Fashe da Dariyar Jin Dadi Yayin da Ake Yi Masa Susan Kunne

“Tsoho Ya Dawo”: Karamin Yaro Ya Fashe da Dariyar Jin Dadi Yayin da Ake Yi Masa Susan Kunne

  • Wani yaro mai ban dariya ya tsinci kansa a aljannar duniya yayin da mahaifiyarsa ke goge masa dattin kunne
  • A cikin bidiyon, abun susa kunnen da aka zura wa yaron a kunne yana ta yi masa cakulkuli, inda ya dungi dariya ba kakkautawa
  • Karara ya nuna yana jin dadin yanayin da ya riski kansa a ciki, kuma yadda ya dunga dariya da rufe idanu ya ba masu amfani da soshiyal midiya dariya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani dan jinjirin yaro ya ja hankalin masu amfani da dandalin soshiyal midiya saboda yadda ya dunga dariya a wani bidiyo da ya yadu.

A cikin bidiyon da @junettepetitfrere0 ta wallafa a TikTok, an gano inda ake gogewa yaron kunne da abun susa kunne.

Kara karanta wannan

Bidiyon Zakzaky yana magana kan harsashi 38 da likitoci suka gano a kwakwalwarsa ya yadu

Yaron da ake gogewa kunne
“Kakanni Sun Dawo”: Karamin Yaro Ya Fashe da Dariyan Dadi Yayin da Ake Yi Masa Susan Kunne Hoto: TikTok/@junettepetitfrere0.
Asali: TikTok

Ga dukkan alamu, abun susa kunnen na ta yi masa cakulkuli, saboda haka ya dungi dariya cikin yanayi na farin ciki da ke nuna lallai yana jin dadin abin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kai har ya dunga lumshe idanu kamar wani mai jin bacci saboda dadin da yake ji.

Yanayin yadda yaron ke dariya kamar wani babba ya sanya wasu 'yan TikTok kiransa da sunan kaka.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Ani Save ya ce:

"Tsoho 'dan shekaru 70."

@Lioness ya yi martani:

"Ya yi kama da Alhajin birni."

@Igor Takou ya ce:

"Uba a takalmin yaro."

@Andy Andy ya ce:

"Wannan yaron a sama yake."

@Bargheriano ya ce:

"Kina nunawa budurwarsa ta gobe lagon wannan hadadden yaron."

@D̲E̲V̲E̲L̲O̲P̲A̲ G̲H̲ ya ce:

"Ina ganin mutumin nan ya taba zuwa duniya."

Karamar yarinya da aka tsinta ta zama shar da ita

Kara karanta wannan

Jerin 'yan wasan kwallon kafa 10 da aka taba yankewa hukuncin dauri da laifukan da suka aikata

A wani labarin kuma, wani matashi dan Najeriya da ya tsinci yarinya a bola watanni da suka gabata ya yi karin haske kan rayuwar yarinyar.

Bawan Allah mai suna, Ben Kingsley Nwashara, ya tsinci yarinyar da wata da ba a san kowacece ba ta yasar sannan ya dunga kula da ita tun daga lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel