“Ba Ta Siyarwa Bace”: Uba Ya Mayarwa Ango da Kudin Sadakin Diyarsa, Ya Yi Magana 1 Mai Ratsa Zuciya

“Ba Ta Siyarwa Bace”: Uba Ya Mayarwa Ango da Kudin Sadakin Diyarsa, Ya Yi Magana 1 Mai Ratsa Zuciya

  • Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuno wani uba 'dan Najeriya yana mayar da sadakin auren diyarsa ga dangin angon
  • Mutumin ya yi bayanin cewa al'adar Yarbawa ne mayar da sadakin amarya, kasancewar ba siyar da diyarsa zai yi ba
  • Ya kuma sanyawa angon albarka tare da yi masa fatan alkhairi wajen kula da amanar da aka ba shi wato amaryarsa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Daya daga cikin bidiyoyi mafi shahara a TikTok a yan kwanakin nan ya nuno wani uba 'dan Najeriya wanda ya bai wa dangin ango mamaki ta hanyar mayar masu da kudin sadakin da suka biya na auren diyarsa.

Mahaifin amaryar, wanda ya kasance Bayarabe, ya yi bayanin cewa a al'adarsa mayar da kudin sadakin amarya, wata alama ce ta girmamawa da godiya.

Kara karanta wannan

Wani uba ya yi watsi da 'yan kai amarya, ya yi wa diyarsa rakiya zuwa dakin mijinta da kansa, bidiyo

Uba ya mayar da sadakin diyarsa
“Ba Ta Siyarwa Bace”: Uba Ya Mayarwa Ango da Kudin Sadakin Diyarsa, Ya Yi Magana 1 Mai Ratsa Zuciya Hoto: @preciousbee_alaga/TikTok
Asali: TikTok

Ya bayyana cewa ba siyar da diyarsa ya yi ba, illa ya bayar da ita cike da soyayya da farin ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan sai ya yi wa angon addu'ar samun wadata da nasara a rayuwa, domin ya kula da diyarsa da kyau.

A cikin bidiyon @preciousbee_alaga, dangin angon, wadanda karamcin mahaifin amaryar ya taba su, sun karbi kudin sadakin cike da godiya sannan suka gode masa kan wannan karamci da alkhairi nasa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Nemanltreats ya rubuta:

"Hakan na nufin iyayenta ba siyar da ita za su yi ba, yana nufin tana iya zuwa gida ba tare da tsoron komai ba."

EricJohnikenna:

"Ya kamata a soke sadaki da gaske. Siyarwa ne ko mutane su yarda ko kada su yarda."

Centralvawulence:

"Hakan ya kasance ne saboda idan wani abu ya samu yarinyar, sai a dawo da gawarta gidan mahaifinta."

Kara karanta wannan

Hazikin matashi ya kera otal da katafaren gida daga kwalaye, bisararsa ta burge mutane

Fave:

"Hakan na nufin diyarsu ba ta siyarwa bace."

Mrsldahosa:

"Idan suka yi aure a Amurka basa biyan sadaki."

Lilly Beauty:

"Ba a mayar da sadaki idan kana ganin ya yi yawa sai ka dauki kadan sannan ka mayar da sauran haka 'yan kabilar Ibo suke yi."

Malami ya yi fatawa kan sadaki

A wani labarin, mun ji cewa Ibrahim Khalil wanda babban malamin addinin musulunci ne ya shiga labarai saboda wata fatawa da ya bada.

An yi wa Sheikh Ibrahim Khalil tambaya a game da mafi karancin sadaki, abin mamaki sai ya bada amsa da N20, 000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel