An Kwashi ’Yan Kallo Yayin da Ango da Amarya Suka Kira ’Yan Sanda Aka Kama Mai Rabon Abinci

An Kwashi ’Yan Kallo Yayin da Ango da Amarya Suka Kira ’Yan Sanda Aka Kama Mai Rabon Abinci

  • Wani faifan bidiyo ya nuna wata dirama da aka tafka a wajen daurin aure bayan da aka kama wata mai rabon abinci tana satar abincin bikin
  • An jefa baƙi da masu fatan alheri cikin tsananin mamaki bayan an gano abin da ya faru da abincin da aka ware masu
  • Yayin da wasu masu amfani da yanar gizo suka nuna rashin jin dadin yadda aka kama mai rabon abincin, wasu kuma sun goyi baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

An shiga rudani a wajen wani biki yayin da aka kama wata mai rabon abinci da laifin satar abincin da ma'auratan suka siya don rabawa baki.

A cewar @favour_gist, mai rabon abincin ta hana bakin da aka ce ta kaiwa, ta boye da zummar guduwa da shi.

Kara karanta wannan

An cafke mutane 5 da ‘sace’ buhuna 1800 na abincin ‘yan gudun hijira a Kano

An gano yadda mai rabon abincin ta boye abincin da aka don baki.
An gano yadda mai rabon abincin ta boye abincin da aka don baki. Hoto: @favour_gist
Asali: TikTok

Akan yadda aka bankado mugun nufin mai rabon abincin, wata muryar mace a cikin faifan bidiyon @favour_gist ta bayyana cewa an yanka shanu uku a wajen bikin auren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokacin da aka fahimci mutane da yawa ba su samu abincin ba, sai aka fara yin bincike har aka gano inda ta boye abincin a wasu manyan kuloli.

Mutane sun yi sharhi kan wannan bidiyo da ya yadu a shafin TikTok.

Kalli bidiyon da ke a ƙasa:

Abin da mutane ke cewa:

Mummy J ta ce:

"Na san akan dan debi abincin kadan a kai gida kamar yadda aka saba, ga shi garin son banza sun ja an kama su."

Nas ta ce:

"A bikina ba zan damu da wanda ya saci abinci ba, ma damar ina cikin farin ciki a wannan ranar."

Kara karanta wannan

Abuja: Mota ta murkushe barawo bayan fauce kayan abincin wata mata, ya shiga kakani-kayi

Maks ya ce:

"Ni wanda na gani, mai rabon abinci ta cika babbar kula da soyayyen kaza. Lokacin da za ta je ta saka a bayan motamutane suka kama ta."

teefah_ ta ce:

"Zan hada sojoji tare da masu raba abinci a ranar bikin aure na. Na ga ta yadda za ka boye abinci a ranar."

Tsadar abinci: An gudanar da zanga-zanga a jihar Oyo

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa maza da mata sun fita zanga-zagar lumana a jihar Oyo don nuna adawa kan tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya.

Masu zanga-zagar sun nemi shugaban kasa Bola Tinubu da ya tuna da irin alkawurran da ya dauka lokacin yakin neman zabe na cewar talaka zai ji dadi a mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel