Shugaban Kasa Ya Fitar da Sababbin Nadin Mukamai a Hukumomin NCC, NIGCOMSAT da BB

Shugaban Kasa Ya Fitar da Sababbin Nadin Mukamai a Hukumomin NCC, NIGCOMSAT da BB

  • Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin shugabanni da-dama da za su kula da hukumomi da kamfanoni a ma’aikatar sadarwa
  • An fito da sunayen darektoci, kwamishinoni da shugabannin da aka nada ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani
  • A madadin shugaban kasa, Ajuri Ngalale ya ja hankalin wadanda aka ba mukamai a NCC, NIGCOMSAT da Galaxy Back Bone Ltd

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya amince da wasu nade-naden mukamai a ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani.

Sanarwa ta fito daga fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, inda aka ji cewa an nada darektoci da kwamishononi a wasu hukumomi.

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya nada mukamai a ma'aikatar tarayya a Abuja Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya nada shugabannin Galaxy Back Bone

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: Tinubu ya nada sabon shugaban AMCON da aka yi waje da Ahmed Kuru

Kamar yadda jawabin da Ajuri Ngalale ya fitar ya bayyana, an nada Opeyemi Dele-Ajayi ya jagoranci cibiyar Bridge da ke karkashin NCC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nade-naden ya shafi kamfanin Galaxy Backbone da yake hannun gwamnatin tarayya, an nada Farfesa Ibrahim Adepoju Adeyanju.

Sanarwar ta fito watanni hudu da nada shugabannin NCC, NIPOST, NITDA da sauransu.

Shugabannin Hukumar NCC

(1) Abraham Oshadami — Kwamishinan harkokin fasaha

(2) Rimini Makama — Kwamishinan kula da masu ruwa da tsaki

(3) Opeyemi Dele-Ajayi — Shugaban cibiyar fasahar zamani ta Bridge

Shugabannin Hukumar NIGCOMSAT

(1) Abiodun Attah — Babban darektan harkokin fasaha

(2) Aisha Abdullahi — Babbar darektar kudi da gudanarwa

(3) Jaiyeola Awokoya — Babban darektan talla da cigaban kasuwanci

...Kamfanin GALAXY BACKBONE (BB) LIMITED

(1) Ibrahim Adepoju Adeyanju — Babban Darekta/Shugaba (CEO)

(2) Mohammed Sani Ibrahim — Babban Darektan harkokin kudi

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta karbe Naira Biliyan 1.5 daga hannun tsohon shugaban hukumar NIRSAL

(3) Olusegun Olulade — Babban Darektan Kula da abokan hulda da talla

(4) Olumbe Akinkugbe — Babban Darektan Fito da Fasahar zamani

Bola Tinubu ya yi kira na musamman

Ajuri Ngelale ya ce shugaba Bola Tinubu yana sa ran cewa wadannan kwararru da aka zakulo za su bunkasa tattalin arzikin zamani.

Ana fatan sababbun shugabannin za su taka rawar gani wajen kawo cigaba a Najeriya.

Shugaban kasa ya nada shugaban AMCON

Dazu nan aka samu labari cewa Mista Gbenga Alade aka zaba ya zama sabon shugaban hukumar AMCON mai kula da kadarorin kasa.

Shugaban kasa ya sallami Malam Ahmed Kuru wanda Muhammadu Buhari ya nada tun a 2015, a Disamban 2020 ne aka sabunta wa’adinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel