Fitacciyar Jarumar Fina-Finai a Najeriya Ta Bayyana Amfanin Saduwa Kafin Aure, Ta Tona Asirin Mata

Fitacciyar Jarumar Fina-Finai a Najeriya Ta Bayyana Amfanin Saduwa Kafin Aure, Ta Tona Asirin Mata

  • Jarumar fina-finan Nollywood, Tosin Adekansola ta bayyana ra’ayinta kan kwanciya kafin masoya su yi aure
  • Tosin ta ce ta na goyon bayan saduwa kafin aure saboda hakan zai kara dankon soyayya da kuma sanin halin juna
  • Adekansola ta bayyana haka a cikin wata hira da Debbie Shokoya inda ta fadi yadda mata ke cin amanar mazajensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Tosin Adekansola ta bayyana matsayarta kan saduwa kafin aure.

Tosin ta ce ya kamata masoya su san junansu kafin yin aure wanda rayuwa ce ta har abada.

Jarumar fina-finai ta bayyana ra'ayinta kan kwanciya kafin aure
Fitacciyar Jarumar Fina-Finai, Tosin Adekansola Ta Bayyana Amfanin Saduwa Kafin Aure. Hoto: Tosin Adekansola.
Asali: Facebook

Mene Tosin ke cewa kan aure?

Jarumar ta ce yin hakan zai kara tabbatar da ginin soyayyarsu don ta inganta da samun rayuwar aure ta har abada, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Ku taimaka mun: Yar Najeriya da ke karatu a UK na neman naira miliyan 17.6 don biyan kudin makaranta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kuma ce hakan zai kara dankon zumunci da soyayya da fahimtar juna da kuma sanin abin da mutum ya fi so a wurin masoyinsa.

Ta kara da cewa kwanciya kafin aure zai inganta lafiar masoyan da kara dankon soyayya wanda idan ba su kwanta kafin auren ba hakan ba zai samu ba.

Shawarin da jarumar ta bayar

Adekansola ta fadi haka a cikin wata hira da Debbie Shokoya inda ta bayyana yadda mata ke cin amanar mazajensu ta hanyar saduwa.

Har ila yau, Tosin ta ce kwanciya kafin aure zai bai wa mutum damar sanin girman sha’awar abokin zamansa ba tare da samun matsala ba.

Ta ce:

“Saduwa kafin aure ya na da kyau saboda mata da yawa su na cin amanar mazajensu saboda ba sa iya gamsar da su.”

Ta ce mafi yawan matan su na fita neman maza a waje wanda sanin halinsu kafin auren ya na da tasiri kan haka, The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini ya gargadi Tinubu yayin da aka sace shugaban PDP, ya hango sabuwar matsala

Hotunan Hadiza Gabon sun ta da kura

Kun ji cewa Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, ta haddasa cece-kuce a kafafen sadarwa bayan ta saki wani sabon hotonta.

A baya dai jarumar ta kasance irin dirarrun matan nan wadanda ake kira da yan duma-duma amma hoton da ta sake yanzu ya bar baya da kura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel