“Na Siya Bokitin Shinkafa 1 Kan N3,000”: Matashiya Ta Gano Kauyen da Ake Siyar da Shinkafa Mai Sauki

“Na Siya Bokitin Shinkafa 1 Kan N3,000”: Matashiya Ta Gano Kauyen da Ake Siyar da Shinkafa Mai Sauki

  • Wata matashiya ta ce ta gano wani kauye a jihar Enugu inda ake siyar da shinkafa a farashi mai rahusa, N3,000 kowani bokiti daya
  • A wani bidiyo da ta wallafa a Nuwamban 2023, matashiyar, Anasthesia Michael, ta yi ikirarin cewa kasuwar kauyen na ci ne sau hudu duk shekara
  • Anasthesia ta ce ta siyawa kanta bokiti biyu, amma mutane a sashin sharhi sun nuna shakku kan labarin nata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata matashiya 'yar Najeriya ta ce ta siya bokitin shinkafa daya kan N3000 a kasuwar wani kauye a jihar Enugu.

A wani bidiyo da ta wallafa a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2023, Anasthesia Michael ta ce abubuwa na da arha sosai a lokacin da ta ziyarci kasuwar.

Kara karanta wannan

An debi garabasa: Jama'a sun mamaye 'dan kasuwa bayan da ya samar da shinkafa mai sauki, buhu N58k

Matar ta ce ta siya bokin shinkafa kan N3k
“Na Siya Bokitin Shinkafa 1 Kan N3,000”: Matashiya Ta Gano Kauyen da Ake Siyar da Shinkafa Mai Sauki Hoto: @annastasia_michael.
Asali: TikTok

Mutane a sashinta na sharhi sun tirke ta kan lallai sai ta fadi sunan kasuwar, kuma sai ta ce a Afia Nkwo ne amma bata fadi ainahin wajen ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce kasuwar na ci ne sau hudu a duk shekara kuma cewa shinkafar da ta siya mai dadi ce.

Mutane sun nuna shakkun kan ikirarin Anasthesia

Duba ga tsadar shinkafa da sauran kayan abinci a Najeriya a yanzu haka, mabiyanta da dama sun nuna shakku kan abin da ta ce sannan sun zarge ta da fadar karya.

Sun dage cewa ba abu ne mai yiwuwa ba siyar da bokitin shinkafa kan N3000 koda kuwa a watan Nuwamban 2023 ne.

Amma dai daya daga cikinsu ta yi ikirarin cewa ta san kasuwar kuma cewa gaskiya Anasthesia ke fadi.

Da yake magana da jaridar Legit, wani 'dan kasuwar shinkafa kuma manomi, Haidar Abdullahio Gadumawa, ya nuna shakku cewa ana iya samun bokitin shinkafa kan N3k.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Benue za ta kori Fulani makiyaya daga jihar ta kan wani dalili 1 tak

Sai dai kuma, ya ce samun shinkafa a farashi mai sauki abu ne mai yiwuwa idan mutum zai siya ne a yankunan karkara, kamar yadda Anasthesia ta yi ikirari.

Haidar ya ce:

"Bana tunanin za ka iya samun shinkafa mai kyau irin wannan kan N3k. Eh, 2023, bana tunanin abu ne mai yiwuwa."

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a kan ikirarin matashiyar

@SOFTMIND DIGITAL ta ce:

"Ba zai taba yiwuwa ba a siya shinkafa bokiti daya N3,000 a ko'ina a Najeriya, mu dunga fada ma kanmu gaskiya don Allah."

@user93588041173743 ya yi martani:

"Wani kasuwa don Allah?"

@Harmony Emirates ta ce:

"Gaskiya kike fadi na san wannan wurin, ko a wurin da nake ya fi arha amma ba a kasuwa muke siya ba muna noma namu ne."

@THE GREAT IROKO ya ce:

"Wurin nan jihar Ebonyi ne amma kusa da jihar Enugu sosai. Mutanen Enugu suna siya daga wajen."

Kara karanta wannan

An kai karar Sunusi Lamido ga Tinubu kan bala'in da ke tunkarar Kano kan masarautu, an fadi dalili

Matashi ya baje kolin shinkafarsa mai arha

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani 'dan kasuwa ya bayyana cewa yana siyar da kowani buhun shinkafa kan N58,000, kuma cewa yana iya kai wa mutum duk inda yake a fadin Najeriya.

Haidar Abdullahi Gaduwama ya tallata haajarsa a dandalin X, kuma akwai mutane da dama da suka bibiyi shafinsa, suna masu nuna ra’ayinsu na son siya a wajen sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel