Dakarun Noma: Gwamnati Ta Dauki Mataki 1 Na Tsare Manoma Daga Farmakin ’Yan Bindiga
- Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar kaddamar da dakarun tsaron gonaki don ba manoma kariya daga hare-haren 'yan bindiga
- Majalisar zartaswa ta tarayya ce ta cimma wannan matsayin a taronta na 139 da ta gudanar bisa jagorancin Kashim Shettima
- Murtala Sani, wani manomi daga yankin Faskari inda matsalar tsaro ta fi ƙamari a Katsina, ya yi maraba da dakarun noma, tare da jan hankali
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC) ta amince da rabawa manoma takin zamani a saukake tare da kuma kaddamar da dakarun gona don yaƙi da 'yan ta'adda da ke farmakar manoma.
Majalisar ta ce daukar wadannan matakan za su taimaka ainun wajen magance karancin abinci, tsadar abinci, yunwa da rage matsin tattalin arziki.
Stanley Nkwocha, babban mai hidimtawa shugaban ƙasa Bola Tinubu ta fuskar watsa labarai, ofishin mataimakin shugaban kasa ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nkwocha ya fitar da sanarwar ne jim kadan bayan kammala taron majalisar na 139 wanda aka yi shi ta intanet bisa jagorancin Kashim Shettima, The Cable ta ruwaito.
Kokarin da gwamnati za ta yi wa manoma
A yayin taron, Shettima ya yi nuni da cewa idan har aka samar da tsari mai kyau, Najeriya za ta cimma gagarumar nasara nan kusa.
Abubakar Kyari, ministan noma da samar da abinci a yayin taron, ya ce gwamnati za ta gana da kamfanonin sarrafa taki irinsu Indorama, Dangote da Notore.
An cimma matsayar cewa gwamnonin jihohi za su horas da manoma hanyoyin noma na zamani da zai bunkasa noman don samun amfanin gona mai kyau.
Gwamnati za ta fitar da abinci don karya farashi
Majalisar ta kuma amince da kirkirar rundunar daji ta wucin gadi, yayin da gwamnati ke kokarin kaddamar da 'yan sandan jihohi duk don magance barazanar tsaro da manoma ke fuskanta.
Business Day ta ruwaito gwamnatin na kuma duba yiwuwar fitar da ton 42,000 na abinci daga rumbun abinci na gwamnati don karya farashin abincin a kasuwa.
Ministan ya yi kira da a dauki mataki kan 'yan kasuwar da ke fakewa da dala ta tashi suna kara kudin kaya kamar takin 'Urea' wanda ke jawo koma baya ga harkar noma.
Dakarun noma: Sai gwamnati ta yi da gaske za ta cimma nasara
A zantawarsa da Legit Hausa, Murtala Sani, wani manomi daga shiyyar Funtua, da ta haɗa da Funtua, Faskari, Dandume da Sabuwa a jihar Katsina, ya yi maraba da dakarun noma.
Shiyyar Funtua, musamman yankin Faskari su ne kan gaba a garuruwan da matsalar tsaro ta fi ta'azzara a jihar Katsina, inda a wasu garuruwan ma aka daina noman kwata-kwata.
Murtala Sani ya ce:
"Idan har da gaske gwamnatin take yi to abu ne mai kyau. Matsalar kar abun ya zama kamar fadi a baki ne kawai amma babu aikatawa.
"Yanzu kamar a yankunan Faskari, manoma sun hakura da noman gaba daya, saboda 'yan bindiga na kwace gonakin wasu kuma ayi garkuwa da su."
Sani ya yi nuni da cewa idan har aka tura jami'an tsaro gonaki kamar yadda gwamnatin ta ce, to hakan zai sa abinci ya wadata kuma a fita daga wannan matsin tattalin arzikin.
Mahangar Murtala kan 'yan sandan jihohi
Ko da aka tambaye shi mahangarsa kan 'yan sandan jihohi' da ake kokarin kirkiro wa a Najeriya, Sani ya ce yana fargabar gwamnoni su mayar da su karnukan farautarsu.
Ya ce mafi akasarin masu goyon bayan 'yan sandan jihohi gwamnoni ne masu ci, saboda tsarin daukar aiki da biyan albashi zai rataya a wuyansu, don haka sai yadda suka so za a yi.
"Idan ka ga ana samun sabani tsakanin kwamishinan 'yan sanda da gwamnatin jiha, to ya ƙi yin abin da suke so, wannan ma'aikacin tarayya ke nan.
"Ina kuma ga gwamnatin jihar ce ta dauke su aiki, kuma ta ke tsara abin da za su yi? Ka ga za su zama sai abin da gwamnan ke so za ayi, karshe za su koma 'yan amshin shata kawai."
Dangote ya ce babu hannunsa a tsadar abinci a Najeriya
A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito cewa Hajiya Fatimah Aliko Dangote, ta ce babu sa hannun kamfanin Dangote a tsadar kayan abinci a kasar.
Hajiya Fatimah ta bayyana hakan ne biyo bayan yadda wasu ke zargin kamfanin da tsawwala kudin kayan abinci, inda ta ce yanzu Dangote ba ya sarrafa kayan abinci kwata-kwata.
Ta bayyana cewa sukari, gishiri da kayan hadi ne kawai kamfanin Dangote ke sarrafa wa amma tun shekaru biyar baya ta sayar da kamfanin Olam wanda a baya yake sarrafa kayan fulawa.
Asali: Legit.ng