Kamfanin Dangote Ya Nesanta Kansa Daga Hannu a Tsadar Kayan Abinci a Najeriya

Kamfanin Dangote Ya Nesanta Kansa Daga Hannu a Tsadar Kayan Abinci a Najeriya

  • Kamfanin Dangote ya warware rade-radin da ake yi na cewar kamfanin na da hannu a tsadar kayan abinci da ake fama da ita a kasar
  • Hajiya Fatimah Aliko Dangote, babbar darakta a kamfanin ta ce a halin yanzu babu wani kayan abinci da kamfanin ke sarrafawa
  • Fatima ta ce tun shekaru biyar baya Dangote ya sayar da kamfanin sarrafa abincinsa na Olam, don haka ba su da hannu a tsadar kayan abinci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Aliko Dangote ya bayyana cewa babu sa hannun rukunoni kamfanonin Dangote a tsadar kayan abinci da ake fama da su a Najeriya.

Ta bakin Hajiya Fatima Aliko Dangote, babbar darakta a rukunonin kamfanin, Dangote ya ce shekara biyar kenan da ya sayar da kamfaninsa na sarrafa abinci.

Kara karanta wannan

Kwastam ta fara raba wa talakawan Najeriya kayan abinci da ta kwace, ta fadi ka'idojin cin gajiyar

A kayan abinci, Dangote na sarrafa sukari, gishiri
A kayan abinci, Dangote na sarrafa sukari, gishiri da kayan hadi ne kawai yanzu, in ji Fatima. Hoto: @DangoteGroup
Asali: Getty Images

A tattaunawar ta da BBC, Hajiya Fatima ta ce kamfanin Olam da ke sarrafa kayan abinci da kayan gona a Najeriya yanzu ba ya karkashin ikon kamfanin Dangote.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin Dangote ya daina sarrafa kayan abinci

Ta ce kamfanin Olam a yanzu yana sarrafa fulawa, taliya, semolina da duk wani nau'i na kayan fulawa.

"A yarjejeniyar mu da su, za su ci gaba da amfani da sunan Dangote a kayayyakinsu har zuwa shekarar 2025 da za su daina.
"A kayan abinci, muna sarrafa sukari, gishiri da kayan hadin abinci ne kawai, amma muna shirin fara sarrafa shinkafa a wannan shekarar ko ta gaba."

- A cewar babbar daraktar.

Kamfanin Dangote ba zai iya karya farashi ba?

Fatima ta kara da cewa kamfanin Dangote na adawa da yadda farashin kayan abinci ke hauhawa, tare da fatan abubuwa su yi sauki.

Kara karanta wannan

Tsadar siminti: Gwamnati ta yi barazanar daukar mataki 1 da zai jefa Dangote da BUA cikin matsala

Ko da aka tambaye ta idan za su iya rage farashin kayayyakin su, sai cewa ta yi:

"Ba mu da laifi a karin farashin kaya, muna sayo sukari daga Brazil da dalar Amurka, haka danyen gishiri da sauran su, matsalar da ake fuskanta kenan.
"Kayan hadin siminti ne kawai ake samun su a Najeriya, amma sarrafa shi zai dogara akan amfani da dala, kama daga motoci, iskar gas, tayoyi, da sauran kayan gyara."

Hakazalika ta ce kamfanin Dangote na sayar da siminti akan naira dubu bakwai zuwa dubu takwas sabanin naira dubu 15 da ake sayar da shi a wasu kasuwanni.

Kalli bidiyon tattaunawar a kasa:

Tsadar siminti: Gwamnati za ta dauki mataki kan su Dangote da BUA

A wani labarin ne Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ce za ta buɗe iyakokin kasar don shigo da siminti.

A cewar gwamnatin, shigo da siminti cikin kasar ne kawai zai karya farashin simintin a Najeriya biyo bayan yadda farashinsa ya yi tashin gwauron zabi.

Sai dai gwamnatin ta gargadi kamfanonin sarrafa siminti na cikin gida irin su Dangote, BUA da sauran su da su kuka da kansu idan kasuwar su ta durkushe saboda matakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel