Gwamnoni sun goyi bayan kafa ‘yan sandan jihohi

Gwamnoni sun goyi bayan kafa ‘yan sandan jihohi

- Gwamnan jihar Zamfara ya ce gwamnoni sun goyi bayan kafa 'yansandan jihohi

- Abdulazeez Yari ya ce kafa 'yansandan jihohi zai kawo karshen kalubalen da kasar ke fuskanta a fannin tsaro

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Gwamnan jihar Zamfara Abdulazez Yari, ya ce barin kowa ce jiha ta kafa ‘yansandan ta zai magance matsalar tsaro da ake fuskanta a fadin kasar.

Abdulaziz Yari, ya bayyana haka ne a lokacin rufe taron kwana biyu da aka gudanar akan matsalar tsaro da kasar ke fuskanta

Ya ce “mu ma a yau mun goyi bayan matsayar da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya amince da ita cewa ya goyi bayan kowace jiha ta kafa ‘yan sandan ta.”

Gwamnoni sun goyi bayan kafa ‘yan sandan jihohi
Gwamnoni sun goyi bayan kafa ‘yan sandan jihohi

“Batun kafa ‘yansanda a jihohi shine matsayar da muka cimma a taron da muka gudanar a watan Agusta.

KU KARANTA : Wata kungiya ta kaddamar da shirin yiwa Sanata Shehu Sani kiranye akan sukar gwamnatin Buhari da El-Rufai

“Maganar gaskiya ba za mu iya kula da kare dukiyoyi da rayukan kasar nan daga Abuja ba. Don haka akwai bukatar kafa ‘yan sandan jiha,” Inji Abdulazeez Yari.

Yari ya ce, akwai kusan mutane miliyan hudu a jihar Zamfara, amma jami’an ‘yan sandan da aka tura a jihar ba su wuce 5,000.

Dangane da kudin daukan nauyin ‘yan sandan jihohi, Abdulazeez Yari, ya ce bai zama dole kowace jiha ta kafa ba. Jihohin da suka fi bukatar su kuma su na da karfin daukar nauyin, sune za su kafa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel