Matsin Tattalin Arziki: Shettima Ya Sanar da Lokacin da Tattalin Arzikin Najeriya Zai Farfado

Matsin Tattalin Arziki: Shettima Ya Sanar da Lokacin da Tattalin Arzikin Najeriya Zai Farfado

  • Kashim Shettima, mataimakin shugaban kasa ya yi wa masu zuba hannun jari na gida da na waje samar da yanayi mai kyau don bunkasa tattalin arziki
  • Shettima ya ce Shugaba Tinubu ya himmatu wurin inganta tattalin arziki zuwa nan da watanni 15
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani mai fashin baki kan tattalin arziki game da wannan lamari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi alkawarin cewa tattalin arzikin Najeriya zai farfado nan da watanni 15.

Kashim ya ce Shugaba Tinubu ya himmatu wurin samar da yanayi mai kyau don bunkasa tattalin arzikin kasar.

Kashim Shettima ya bayyana lokacin da tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa
Shettima ya yi martani kan farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya. Hoto: Senator Kashim Shettima.
Asali: Twitter

Wane alkawari Kashim ya yi kan tattalin arziki?

Kara karanta wannan

Matasa na murna yayin da gwamnan PDP ya sanar da biyan dubu 10 ko wane wata ga masu bautar kasa

Shettima ya yi wa masu zuba hannun jari alkawarin mayar da kasar wurin inganta musu tattalin arziki, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a jiya Litinin 27 ga watan Nuwamba yayin karbar bakwancin masu zuba hannun jari.

Daga cikin wadanda su ka halarci taron akwai shugabannin gudanarwa na First Surat Group da kuka masu kamfanin MTN a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Wane martani masu zuba hannun jari su ka ce?

Dakta Ali Maina, shugaban First Surat Group ya ce sun yi amfani da kudaden ribar kamfanin wurin inganta rayuwar 'yan Najeriya, New Telegraph ta tattaro.

A bangarenshi, shugaban kamfanin MTN, Ernest Ndukwe ya ce sun shirya hadaka da gwamnatin Tinubu don taimaka masa a kokarin inganta rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

Kwanaki 6 da dawowa Najeriya, Shugaba Tinubu zai lula kasar Larabawa gobe

A martanin wani mai fashin baki kan tattalin arziki, Lamido Bello ya ce gyara tattalin arziki a watanni 15 zai yi matukar wahala musamman ga su masu zuba jarinsu a kasar.

Ya ce:

"Daidaita tattalin arzikin Najeriya a cikin watanni 15 wanda zai sa har masu zuba jari su iya zubawa zai yi matukar wahala.
"Saboda tarun kalubale na rashin kyawun yanayi wanda masu zuba jari ke kallo da suka hada da rashin tsaro da rashin ingantaccen wutar lantarki da kuma tsadar iskar gas da man fetur,"

Ya ce wadannan matsaloli za su kawo tsaiko saboda duk mai zuba hannun jarinsa riba ya ke so ba faduwa ba.

Tinubu zai sake karbo bashin biliyan 8

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa don sake karbo bashin dala biliyan 8.69.

Tinubu ya kuma bukaci karin yuro miliyan 100 kamar yadda gwamnatin Buhari ya amince a wata Mayun 2023.

Wannan na zuwa ne bayan Bankin Duniya da na raya Afirka sun yi alkawarin tallafawa da karin naira biliyan 2.5.

Asali: Legit.ng

Online view pixel