Bai da Wata Mafita: Tsohon Abokin Siyasar Tinubu Yayi wa Gwamnatin APC Kaca-Kaca

Bai da Wata Mafita: Tsohon Abokin Siyasar Tinubu Yayi wa Gwamnatin APC Kaca-Kaca

  • Dr. Usman Bugaje ya yi tir da kamun ludayin sabuwar gwamnatin tarayya, yana ganin ba a san inda aka dosa ba
  • Tsohon ‘dan majalisar ya soki yadda aka cire tallafin fetur ba tare da wani tanadi ba, ya ce ana aiki babu shawara
  • Bugaje ya shiga tsohuwar ACN wanda ta kunshi jam’iyyun AC, AD da ACD, saboda haka ya san Bola Tinubu tun tuni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Usman Bugaje yana ganin Bola Ahmed Tinubu bai san yadda zai shawo matsalolin da suka dabaibaye kasar nan ba.

Dr. Usman Bugaje ya yi hira da tashar Channels, a nan ne ya soki yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ke jagorantar al’umma.

Tinubu
Usman Bugaje ya soki Bola Tinubu Hoto: Usman Bugaje/@KennedyWandera
Asali: Facebook

Duk kokarin da gwamnati mai-ci ta ke yi na samun saukin tashin dala da hauhawar farashi ba su burge sanannen ‘dan siyasar ba.

Kara karanta wannan

Sanatoci za su kafa kwamitin binciken Buhari kan bashin N30tr da ya ci a CBN

Tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayyan ya ce yanzu an fahimci Bola Tinubu bai san wata dabara da zai yi domin ya ceci kasar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A yau, kowa ya gano cewa Bola Tinubu bai da mafita game da matsalolin kasar nan."
"Gwamnatinsa (Shugaba Bola Tinubu) ta gagara shawo kan muhimman abubuwa."

- Usman Bugaje

Tinubu ya yi garajen cire tallafin fetur

A hirar da aka yi da shi a shirin siyasar talabijin, Usman Bugaje ya zargi gwamnatin Tinubu da cire tallafin fetur ba tare da shiri ba.

Tsohon sakataren na jam’iyyar ACN yake cewa ba a duba tasirin janye tallafin man fetur ba kafin gwamnati tayi watsi da tsarin.

"Ba a fito da tsari ba tare da an duba tasirinsa kuma an shirya abin da zai haifar ba. Amma a zahiri, ya yi wannan ne babu shiri."

Kara karanta wannan

Yaron Tinubu ya ji babu dadi daga rokon mutane a yi hakuri da gwamnatin mahaifinsa

"Mun yi tunani da sabuwar gwamnatin tarayya ta karbi mulki, mun sa rai zai zagaye kan shi da kwararru."
"Mun sa ran cewa da ya sanar da cire tallafin tetur, dole yana da tsarin da zai magance halin da za a shiga."

- Dr. Usman Bugaje

Shugaba Tinubu bai da mashawartan kwarai?

An rahoto Bugaje yana cewa masu ba sabon shugaban Najeriyan shawara ba su fada masa gaskiyar halin da Najeriya ke ciki ba.

Tsohon mai ba mataimakin shugaban kasa shawara a kan siyasa ya ce ‘yan kanzagi suka zagaye Mai girma Bola Tinubu a mulki.

Bugaje ya ce akwai bukatar Tinubu ya nemi wadanda su kan sana bin da suke yi, kuma su ka san halin da talakawa suke ciki.

Gwamnatin Tinubu za ta raba abinci

Dazu aka samu labari Ministan tattalin arziki, Wale Edun ya bayyana shirin da ake yi domin a karya farashin kayan abinci a kasuwa.

Kara karanta wannan

Emefiele: Shugaban majalisa ya ambaci mutumin da ya jefa kowa a matsin tattali

Edun ya ce Bola Tinubu ya amince Gwamnatin tarayya ta fito da karin metric ton 60, 000 da za a rabawa talakawa domin a yaki yunwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel