Bayan Shekaru 2, Dan Gwagwarmayar Kafa Ƙasar Yarbawa Igboho Ya Dawo Najeriya, an Gano Dalili

Bayan Shekaru 2, Dan Gwagwarmayar Kafa Ƙasar Yarbawa Igboho Ya Dawo Najeriya, an Gano Dalili

  • Shahararren mai rajin kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya dawo Najeriya bayan shafe shekaru biyu yana gudun hijira a Jamhuriyar Benin
  • An ruwaito cewa Igboho ya dawo ne domin gudanar da bikin binne gawar mahaifiyarsa, Misis S.A Adeyomo wacce ta rasu kwanan baya
  • Idan za a iya tunawa, Igboho ya arce ya bar Najeriya bayan da hukumar DSS ta fara nemansa ruwa a jallo akan laifin ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Dan gwagwarmayar kungiyar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho, ya komo Najeriya shekaru biyu bayan ya yi gudun hijira zuwa Jamhuriyar Benin.

Ya komo Najeriya ne domin binne mahaifiyarsa, wadda ta rasu a lokacin da yake tsare kuma ya ke fuskantar shari’a a Jamhuriyar Benin.

Kara karanta wannan

Sanata Sani ya fadi mafita 1 da Musulmi da Kiristoci zasu runguma domin farfado da naira

Bayan mutuwar mahaifiyarsa, Igboho ya dawo Najeriya.
Bayan mutuwar mahaifiyarsa, Igboho ya dawo Najeriya. Hoto: Sunday Igboho
Asali: Twitter

Igboho zai gudanar da jana'izar mahaifiyarsa

Wata sanarwa da mai magana da yawun Igboho, Olayomi Koiki, ya fitar a shafin X a ranar Alhamis, 22 ga Fabrairu, ta tabbatar da cewa dan gwagwarmayar ya dawo kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya sanar da cewa:

"Zan iya tabbatar da cewa Cif Sunday Adeyemo yana kan hanyarsa ta zuwa garin Igboho domin yin jana'izar mahaifiyarsa Misis S.A Adeyomo."

Har ila yau, Koiki ya wallafa wani faifan bidiyo wanda aka gano Igboho tare da wasu mutane da ake kyautata zaton suna wurin daukar gawar mahaifiyar ne.

Dalilin da ya sa Igboho ya tsallake zuwa Benin

The Nation ta ruwaito cewa Igboho ya fice daga Najeriya ne a shekarar 2021 zuwa jamhuriyar Benin bayan da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bazama neman sa.

Jami’an DSS sun mamaye gidan Igboho da ke unguwar Soka a Ibadan babban birnin jihar Oyo bisa zargin ta’addanci.

Yayin da yake Jamhuriyar Benin, an kama Igboho ne a lokacin da yake kokarin tafiya Jamus domin haduwa da iyalinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel