An Cafke Mutane 5 da ‘Sace’ Buhuna 1800 na Abincin ‘Yan Gudun Hijira a Kano
- Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun damke wadanda ake zargi sun yi awon gaba da abincin da za a rabawa ‘yan gudun hijira
- Muyiwa Adejobi ya sanar da wannan a ranar Lahadi, yake cewa mutane 5 da ake zargi da danyen aikin sun shiga hannun hukuma
- ‘Yan sanda sun gano buhuna 1, 200 daga cikin 1, 800 da aka sace, kuma ana neman ragowar wadanda suka karkatar da abinci
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun sanar da cewa sun kama buhunan kayan abinci da ya kamata a rabawa ‘yan gudun hijira.
Sanarwar da rundunar ‘yan sanda ta fitar ya bayyana an yi nufin raba wadannan buhunan hatsi ne ga wadanda suka bar gidajensu.
Daga ina aka sato buhunan abincin?
Buhunan sun fito ne daga hukumar UNWFP mai kula da harkar abinci a majalisar dinkin duniya a lokacin da ake kukan tsadar abinci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun sufetan rundunar ‘yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya fitar da sanarwar a ranar Lahadi, ya fadin abin da ya auku.
Muyiwa Adejobi ya ce an dauki kayan abincin daga tashar Ibeto da ke Fatakwal da nufin za a kai su Kano, amma sai aka karkatar da su.
Kakakin jami’an tsaron yake cewa an cafke mutane biyar da ake zargi da laifi a garin Fatawal, wannan ya faru ne tun 6 ga watan Fubrairu.
Bayan an yi ram da wadannan mutane, an yi nasar gano buhuna 1, 238 daga cikinsu. Ana sa ran za a kai su Kano inda ake hana boye abinci.
Jawabin kakakin rundunar 'yan sanda
"Wasu direbobi da aka ba nauyi tare da miyagun masu taimaka masu sun karkatar da buhuna 1, 840 na alkama da aka dauko daga tashar Ibeto a Fatakwal zuwa wani sansanin ‘yan gudun hijira da yake jihar Kano.
"Dakarun (‘yan sanda) sun kama mutane biyar (5) da ake zargi; Umar Hashim, Edidiong Umoh, Udah Stanley, Abubakar Jariri da Yunusa Babangida.
"Kuma an gano 1, 238 na buhunan hatsin da aka sace a motar tare da wata babbar mota da aka yi amfani wajen yin laifin.
"An maida buhunan da aka gano zuwa ga hukumar kula da abinci ta duniya, kuma ana kokarin gano ragowar buhuna 602 da suka bace, sannan a cafke ragowar wadanda ake zargi da laifin."
- Muyiwa Adejobi
Malami ya soki rufe rumbunan abinci
Ana da labari Sheikh Mansur Sokoto bai ganin cewa masu rumbunan abinci suka haifar da tsadar abinci da yunwar da ake ciki a kasar.
Babban shehin ya yi rubutu a Facebook, yake nuna cewa farashin kaya sun tashi ne a sakamakon darajar Naira da bankin CBN ya karya.
Asali: Legit.ng