Sabon IGP Ya Shiga Ofis, Ya Karbi Ragamar Yan Sandan Kasar Daga Hannun Baba

Sabon IGP Ya Shiga Ofis, Ya Karbi Ragamar Yan Sandan Kasar Daga Hannun Baba

  • Sabon mukaddashin shugaban rundunar yan sandan Najeriya, (IGP) Kayode Egbetokun, ya shiga Ofis a hukumance ranar Laraba
  • Tsohon Sifetan 'yan sanda na ƙasa, Usman Alkali Baba, ne ya miƙa masa ragama a hedkwatar hukumar da ke Abuja
  • Egbetokun, ya zama shugaban rundunar yan sanda ta ƙasa na 22 a tarihin bayan naɗin da shugaban kasa, Bola Tinubu, ya masa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Muƙaddashin Sifetan 'yan sandan Najeriya (IGP), Kayode Egbetokun, ya kama aiki a Ofishinsa karon farko a hukumance ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, 2023.

Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa Egbetokun ya karɓi ragamar hedkwatar rundunar 'yan sanda a matsayin IGP na 22 a tarihi.

Sabon IGP ya karɓi ragamar mulki.
Sabon IGP Ya Shiga Ofis, Ya Karbi Ragamar Yan Sandan Kasar Daga Hannun Baba Hoto: vanguard
Asali: UGC

Tsohon shugaban rundunar 'yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya miƙa wa sabon IGP Egbetokun mulki a hukumance da misalin ƙarfe 12:00 na tsakar rana a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Nada Hakeem Odumosu A Matsayin Shugaban Hukumar EFCC? Gaskiya Ta Bayyana

Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ne ya naɗa masa adon zama Sifeta a fadar shugaban kasa, kamar yadda Channels tv ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Na fahimci girman aikin da ke gabana - IGP

Da yake jawabi, mukaddashin IGP na ƙasa ya bayyana cewa ya fahimci girman nauyin da ke tattare da wannan matsayi da aka naɗa shi.

Egbetokun ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki su ba shi haɗin kai kuma su yi aiki kafaɗa-da-kafata, inda ya yi alkawarin cewa zai tafiyar da mulkinsa cikin gaskiya da adalci.

Ya yi fatan cewa zasu ƙara karfafa dangantaka mai kwari tsakanin hukumar yan sanda da sauran hukumomi da kuma zurfafa amfani da fasaha wajen inganta tsaron cikin gida.

Bugu da ƙari, sabon IGP ya yi kira ga 'yan Najeriya su goyi bayan jami'an yan sanda a kokarinsu na kawo karshen aikata muggan laifuka a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Zai Koma Wajen Tinubu a APC? Gaskiya Ta Bayyana

A jawabinsa na bankwana, tsohon IGP, Usman Alkali Baba, yace ya jagoranci rundunar da ta kawo sauyi mai kyau a harkokin tsaron cikin gida.

Gwamna Otu Ya Haramta Aikin Acaba a Babban Birnin Jihar Cross River

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Ribas ya haramta ayyukan 'yan acaɓa a cikin kwaryar birnin Kalaba, babban birnin jihar.

A wata sanarwa da gwamnatinsa ta fitar ranar Laraba, gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne bayan zaman neman shawara da hukumomin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel