Tsadar Abinci: Tinubu Ya Sha Alwashin Daukar Tsattsauran Mataki Akan Kungiyoyin Yan Kasuwa

Tsadar Abinci: Tinubu Ya Sha Alwashin Daukar Tsattsauran Mataki Akan Kungiyoyin Yan Kasuwa

  • Hukumar Gasa da Kare Hakkin Kwastomomi (FCCPC) ta bayyana cewa za ta dauki mummunan mataki a kan kungiyoyin ‘yan kasuwa
  • Shugaban hukumar, Babatunde Irukera shi ya bayyana haka a ranar Talata 18 ga watan Yuli yayin ganawa ta musamman a Abuja
  • Hukumar ta ce daukar matakin ya zama dole ganin yadda kungiyoyin ‘yan kasuwa ke kara fara lokacin da suka ga dama a Najeriya

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya za ta dauki mataki a kan kungiyoyin ‘yan kasuwa saboda zargin kara farashin kaya babu dalili.

Hukumar Gasa da Kare Hakkin Kwastomomi (FCCPC) ita ta bayyana haka ta bakin shugaban hukumar, Babatunde Irukera a ranar Talata 18 ga watan Yuli.

Gwamnatin Tarayya Za Ta Hukunta Kungiyoyin Yan Kasuwa Kan Zargin Kara Farashin Abinci
Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za Ta Hukunta Kungiyoyin Yan Kasuwa Ganin Yadda Suke Kara Farashi Babu Dalili. Hoto: TheCable.
Asali: Twitter

Ya ce suna kara farashin kayayyaki da kuma tsare-tsare da kungiyoyin suke kawo wa wanda ke hana gasa a tsakanin ‘yan kasuwa, TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Tsare Wani Matashi Dan Kwaya Da Ake Zargin Ya Shake Wuyan Mahaifiyarsa Har Lahira

Gwamnatin ta ce za ta dauki mataki a kan kungiyoyin 'yan kasuwa

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Za mu ci gaba da kula da kasuwanni, duk lokacin da muka samu inda aka kara farashin kaya ba dalili ko cutar da mutane masu siyan kaya za mu dauki mataki.
“Wannan shi ne abin da na ce, duk kungiyoyin da suke hada kai don kara farashin kaya, ko kuma su saka doka cewa babu wanda zai dauki kayan abinci idan ba dan kungiyarsu ba, za mu dauki mataki.”

Irukera ya ce wasu kungiyoyin ‘yan kasuwa sun hada wata gungu da zata hana samun gasa a tsakanin ‘yan kasuwa saboda su ci karensu babu babbaka, Punch ta tattaro.

Ta ce hakan ya zama dole ganin yadda farashin kaya ke kara tashi

Ya ce ya zama dole hukumarsu ta dauki matakin gaggawa don dakile hauhawan farashin kaya a kasuwanni bayan shugaban kasa, Bola Tinubu ya sanar da dokar ta baci a harkar abinci, cewar THISDAY.

Kara karanta wannan

An Yi Son Kai: Majalisa Za Ta Binciki Duka Mukaman da Aka Bada a Mulkin Buhari

Ya kara da cewa:

“Hukumar nan ba wai aikinta kadai shi ne kula da manyan kamfanoni ba, ta na kula da ko wane bangare na harkar kasuwanci.
“A kasa irin Najeriya, ya na da wuyan gaske ka iya kula da bangaren kasuwanci da ba sa karkashin hukuma, mafi yawan harkokin kasuwanci a Najeriya da ke kawo kudin shiga ba sa karkashin hukumomi.”

Cire Tallafi: Masu Burodi Sun Shirya Kara Farashi Saboda Tsadar Fulawa

A wani labarin, Kungiyar masu yin burodi a Najeriya sun yi barazanar kara farashi saboda tsadar fulawa.

Shugaban kungiyar masu yin burodi a Najeriya (PBAN) Injiniya Emmanuel Onuorah shi ya bayyana haka yayin ganawa da 'yan jaridu.

Ya ce hakan ya zama dole ganin yadda aka cire tallafin mai da kuma farashin Naira a kasuwanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel