Gwamnan Arewa Ya Shiga Jerin Waɗanda Ƴan Bindiga Ke Shirin Kaiwa Hari, Bayanai Sun Fito

Gwamnan Arewa Ya Shiga Jerin Waɗanda Ƴan Bindiga Ke Shirin Kaiwa Hari, Bayanai Sun Fito

  • Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana cewa yana ɗaya daga cikin abin harin yan bindiga saboda ya hana su rawan gaban hantsi a Katsina
  • Dikko Radda ya faɗi haka ne jim kaɗan gabanin shiga taron tsaro na sirri da ya kira cikin gaggawa kan tsadar rayuwa da kuma ƙalubalen tsaro
  • Ya ce ƙuncin rayuwar da aka shiga a ƙasar nan ya haddasa zanga-zanga a wasu jihohi, don haka ya dace Katsina ta ɗau mataki tun da wuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya kira taron gaggawa na majalisar tsaro ranar Jumu'a, 9 ga watan Fabrairu, 2024.

Gwamna Raɗɗa ya kira wannan taro cikin gaggawa ne domin lalubo hanyoyin magance tsadar rayuwar da ake fuskanta da kuma rashin tsaro a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Birnin tarayya Abuja na fuskantar babbar barazana, majalisar dattawa ta magantu

Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda.
"Ina Cikin Waɗanda Yan Bindiga Ke Son Kai Wa Hari" Gwamna Radda Ya Kira Taro a Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda Ph.D
Asali: Facebook

Taron tsaron wanda gwamnan ya faɗaɗa domin jawo kowa a jiki ya samu halartar Sarkin Katsina, Dakta Abdulmumini Kabir Usman, da sarkin Daura, Dakta Umar Farouq Umar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa sauran mahalarta taron sun haɗa da ƴan kasuwa, shugabannin hukumomin tsaro na jiha da kuma kusoshin gwamnatin Katsina.

Wane mataki Katsina ta ɗauka kan tsadar abinci?

A ɗan takaitaccen jawabin da ya yi kafin shiga taron na sirri, Gwamna Radda ya ce wannan taro ya zama tilas duba da abubuwan da ke faruwar a sassan ƙasar nan.

A cewarsa, ya kira wannan zama ne saboda tsadar rayuwar da ake fuskanta a Najeriya musamman hauhawar farashin kayan abinci.

Ya ce:

"Dukkan mu muna da masaniyar tashin gwauron zabin da farashin kayan abinci ya yi wanda ya haifar da zanga-zanga a jihar Neja, Kano da wasu wurare.

Kara karanta wannan

Kiwon Lafiya: Gwamnan APC ya amince da abu 1, zai ɗauki sabbin ma'aikata sama da 1,000

"Har yanzu bai zo jihar na ba, amma dole mu zauna domin mu gano yadda zamu magance matsalar tun kafin ta fi ƙarfinmu."

Wane gwamna ƴan bindiga ke shirin kaiwa hari?

Game da batun tsaro kuwa, Dikko Raɗda ya ce ƴan bindiga sun bullo da hanyoyin kai hare-hare kan daiɗaikun mutane da kauyuka domin nuna suna nan duk da nasarar da muke samu a kansu.

Gwamna Raɗɗa ya kuma bayyana cewaa daga bayanan sirrin da ya samu, yana ɗaya daga cikin mutanen da ƴan bindiga ke son kai wa hari saboda ya hana su sakat.

Daga nan sai ya bukaci mahalarta taron da su ba da shawarwarin hanyoyin da za a bi don tunkarar lamarin tare da samar da hanyoyin magance matsalar, Vanguard ta tattaro.

Hadimin Gwamnan APC Ya Yi murabus

A wani rahoton mun kawo muku cewa Mai ba gwamnan jihar Sakkwato shawara ta musamman, Buhari Bello Sahhabi, ya yi murabus daga muƙaminsa ranar 7 ga watan Fabrairu, 2024

Tsohon hadimin gwamnan ya miƙa takardar murabus dinsa ga sakataren gwamnatin jihar tare da miƙa godiyarsa ga Allah SWT.

Asali: Legit.ng

Online view pixel