Yadda ‘Yan Sanda Suka Kama Masu Laifi 400 a Jihar APC

Yadda ‘Yan Sanda Suka Kama Masu Laifi 400 a Jihar APC

  • Jami'an 'yan sandan jihar Legas sun kai samame wurare daban-daban da ake zargin ana aikata laifuka a jihar
  • Kakakin 'yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce sun kama mutane 400 da ake zargi da aikata laifuka a yayin samamen
  • Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce za a gurfanar da su dasu gaban shari'a da zaran sun kammala gudanar da bincike a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta ce ta kama kimanin mutane 400 daga wuraren aikata laifuka daban-daban a watan jiya.

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da kamun ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu, ya ce ofishin 'yan sanda 25 ne suka kai samamen.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan Arewa ya sharewa iyalai 70,000 hawaye, ya raba kayan abinci na miliyan 225

'Yan sanda sun kama masu laifi 400
Yadda ‘Yan Sanda Suka Kama Masu Laifi 400 a Jihar APC Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Me yasa aka kama mutanen?

Hundeyin ya ce sun kai samamen ne sakamakon korafe-korafe da bayanan sirri da ke fitowa daga yankunan da aka kama mutanen, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa wasu kwamandojin yanki, sashin RRS da tawagar 'yan sanda masu dabaru na musamman, suma sun bayar da gudunmawa wajen kai samamen.

Kakakin 'yan sandan ya kuma bayyana cewa za a ci gaba da wannan shiri har sai a kakkabe masu aikata laifuka daga jihar.

Ya ce:

"Za a ci gaba wannan samamen har sai an raba jihar Legas da wadannan miyagu."

Ya bayyana cewa za a hukunta wadanda aka kama sannan aka same su da laofi bayan kammala bincike, rahoton Vanguard.

An cafke mai kai wa Turji kaya

A wani labarin, mun ji cewa rundunar ‘yan sanda ta sanar da cafke wani tsohon sojan sama da ke safarar kayan sojoji ga ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama mace da namiji turmi da tabarya a wajen bauta a jihar Arewa

Rundunar ta ce an kama korarren sojan ne wanda ake zargi da samar da kayan sojoji da sauran kaya ga kasurgumin dan ta’adda, Bello Turji.

Tsohon sojan ya na sarafar kayan ne ga ‘yan ta’adda musamman da ke addabar al’umma a jihar Zamfara.

Wanda ake zargin, Ahmed Mohammed ya yi aiki da rundunar a Kaduna na shekaru biyar kacal kafin a kore shi kan wani laifi da ba a bayyana ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel