Omokri Ya Fadi Kwakkwaran Dalilin da Ya Kamata Ya Sa Buhari da Wani Mutum 1 Su Kasance a Gidan Yari

Omokri Ya Fadi Kwakkwaran Dalilin da Ya Kamata Ya Sa Buhari da Wani Mutum 1 Su Kasance a Gidan Yari

  • Reno Omokri, ya bayyana tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya samu lambar zinare a ɓangaren cin hanci a ƙasar nan
  • Omokri ya yi tambaya kan yadda za a fitar da dala miliyan 6.2 daga baitul malin ƙasar nan ƙarƙashin kulawar Buhari ba tare da ya sani ba
  • Hadimin tsohon shugaban ƙasan ya kuma caccaki ɗan uwan ​​Buhari, Sabiu 'Tunde' Yusuf, wanda ya ce "ya kamata ya sanyaya ƙafarsa a gidan yarin Kuje"

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Reno Omokri, wanda ya taɓa zama mataimaki na musamman kan kafafen sada zumunta ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kamata ya fuskanci shari’a.

Kara karanta wannan

"Ba a kyauta mana": Soja ya fusata kan kyautar da Tinubu ya yi wa 'yan wasan Suoer Eagles

Omokri ya ce kamata ya yi gwamnatin Bola Tinubu ta tuhumi Buhari bisa rawar da ya taka wajen taɓarɓarewar da tattalin arziƙin Najeriya ya yi.

Omorki ya magantu kan kulle Buhari
Ana zargin dai an tafka cin hanci da rashawa a karkashin Buhari Hoto: @Mbuhari
Asali: Twitter

Buhari ya sanya kansa a matsayin sarkin yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, amma ana kyautata zaton an tafka cin hanci a gwamnatinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Omokri ya ce kan Buhari da Sabiu Tunde?

Hakazalika Omokri ya bayyana ra'ayinsa na cewa ɗan uwan Buhari, Sabiu Yusuf (Tunde), "ya kamata ya kasance a gidan yarin Kuje" - tare da tsohon shugaban na Najeriya.

Kalaman Omokri dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin an cire dala miliyan 6.2 daga babban ɓankin Najeriya (CBN) ƙarƙashin jagorancin Godwin Emefiele a shekarar 2023.

Omokri ya rubuta shafinsa na X cewa:

"Abdulsalami (Abubakar) shi ne uban dimokuradiyyar Najeriya. Obasanjo (Olusegun) shi ne uban Najeriya ta zamani.

Kara karanta wannan

Atiku ya raba gari da wani na kusa da shi, ya bayyana dalilansa

"Jonathan shine fuskar dimokuradiyya a Afirka. Yayin da Buhari shi ne gwarzo wajen cin hanci da rashawa a Najeriya.
"Ta yaya za ka kasance shugaban ƙasa, kuma za a cire dala miliyan 6.2 daga cikin baitul malin da ke ƙarƙashinka, kuma ba za ka sani ba? Ko dai kai mara amfani ne, ko mai cin hanci da rashawa ne ko kuma duka biyu!
"Ya kamata ace mutumin nan yana can yana sanyaya ƙafarsa a gidan yarin Kuje tare da ɗan uwansa mai sanya agogon Patek Phillipe Nautilus wanda tsohon mai sayar da katin waya ne, Tunde Sabiu Yusuf. Su duka biyun sun yi kama da Anini da Monday Osunbor.

Omokri ya caccaki ɗan uwan Buhari

A wani rubutun kuma, Omokri ya kuma bayyana cewa:

"Ɗan uwan Janar Buhari, Tunde Sabiu Yusuf, ya kasance mai sayar da katin waya a Daura a shekarar 2015. Don Allah a duba a gani ko gaskiya na faɗa, duk da haka, idan ka zura ido a kan wannan hoton, za ka ga cewa Sabiu na sanye da agogon hannu na $99,000 na Patek Phillipe Nautilus.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bayyana alfanun da aka samu sakamakon rufe rumbunan masu boye abinci

"Jimillar albashinsa a shekara a matsayin mataimaki na musamman ga Buhari bai kai $6,000 ba.
"Ta yaya zai iya samun irin wannan agogon yayin da doka ta hana ma’aikatan gwamnati karɓan kyaututtukan da suka wuce dala 250 kuma ba za su iya gudanar da kasuwanci na ƙashin kansu ba yayin da suke kan mulki?
"Don Allah a sake dubawa a ga ko na faɗi gaskiya: An kori wani ministan mai na Najeriya Tam David West tare da gurfanar da shi gaban kuliya saboda karɓar irin wannan agogon a matsayin kyauta.
"Tunde Sabiu da kawunsa Buhari ya kamata su kasance a ɗaure suna fuskantar shari'a. Godwin Emefiele bai kamata ya zama wanda za su ɗora wa laifi ba!"

Boss Mustapha Ya Bada Shaida Kan Emefiele

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bada shaida a gaban kotu kan Godwin Emefiele.

Mustapha ya bayyana yadda aka cire $6.2 daga bankin CBN ta hanyar yin amfani da sa hannun jabu na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel