CCTV ta Nuno Emefiele da Boss Mustapha Suna Jan Kudi $6.2m Daga CBN? Tsohon SGF Ya Yi Martani

CCTV ta Nuno Emefiele da Boss Mustapha Suna Jan Kudi $6.2m Daga CBN? Tsohon SGF Ya Yi Martani

  • Boss Mustapha, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, ya karyata batun kasancewa da hannu a zargin cire dala miliyan 6.2 daga CBN a gwamnatin Buhari
  • Wani rahoto ya yi ikirarin cewa Mustapha da tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele sun bayar da izinin cire kudin inda suka fake da kula da yan kasar waje masu sanya ido a zabe
  • Sai dai kuma, Mustapha ya yi watsi da zarge-zargen, inda ya kira su da abun takaici da rashin tushe, sannan ya nemi a gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Boss Mustapha, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, ya karyata zargin kasancewa da hannu a cire kudi dala miliyan 6.3 ba bisa ka'ida ba daga babban bankin Najeriya (CBN) a gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban APC ya faɗi mataki 1 da Buhari Ya ƙi ɗauka wanda ya sa Tinubu a tsaka mai wuya

Wani rahoton yanar gizo ya yi ikirarin cewa wani mai bincike na musamman da Shugaban kasa Bola Tinubu ya dauka ya bankado badakalar, wanda ya afku yan makonni kafin babban zaben shugaban kasa.

Boss Mustapha ya nesanta kansa dag badakalar kudin CBN
CCTV ta Nuno Emefiele, Boss Mustapha Suna Jan Kudi $6.2m Daga CBN? Tsohon SGF Ya Yi Martani Hoto: @BashirAhmaad, @GodwinIEmefiele
Asali: Twitter

Rahoton ya kuma yi zargin cewa Mustapha da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, sun ba da izinin cire kudin daga asusun bankin da sunan kudin kula da yan kasar waje masu sanya ido a zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewar kamarar CCTV ta dauki yadda aka fitar da kudin daga babban bankin kasar.

Ikirarin karya - Boss Mustapha ya yi martani

Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, Mustapha ya karyata zargin, inda ya kira su da "abin takaici kuma mara tushe."

Ya bayyana labarin a matsayin wanda aka kitsa a kokarin da ake yi na kashe dabi'unsa da bata masa suna.

Kara karanta wannan

Binciken da aka yi a CBN ya bankado abubuwan da Emefiele ya aikata lokacin Buhari

Tsohon SGF din ya ce bai san komai ba game da batun "umarnin shugaban kasa" da aka ambata a cikin rahoton a matsayin dalilin cire kudin, rahoton Guardian Nigeria.

Mustapha ya kuma musanta cewa yana da hannu a tattaunawa ko hada-hadar kudi da suka shafi biyan kudi kan masu kula da ido a zabe.

"A gaskiya, ba ni da masaniya game da irin wannan umarni, kuma ban taba shiga wata tattaunawa kohada-hada dangane da zargin biyan masu sa ido kan zabe na kasar waje ba," in ji tsohon SGF.

Boss Mustapha ya bukaci a yi cikakken bincike

A halin da ake ciki, Mustapha ya kuma yi kira da a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.

Ya bukaci jama’a da kafafen yada labarai da su rika yin tunani mai zurfi sannan kada su karbi labarin da ba haka yake ba.

“Ba ni da wani abun boyewa kuma ina maraba da duk wani sahihin bincike da zai yi karin haske kan gaskiya,” in ji Mustapha.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya rabawa ma'aikata N100,000 don bikin kirsimeti

An bankado wani kulli a CBN

A wani labarin, mun ji cewa rahoton binciken da aka yi kan babban bankin Najeriya na ƙara bayyana yadda tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ci karensa babu babbaka.

Wata badaƙala da aka sake bankaɗowa ta nuna cewa ana zargin Emefiele ya yi amfani da wasu mutane a matsayin wakilai wajen siyen bankin Union Bank of Nigeria (UBN).

Asali: Legit.ng

Online view pixel