Tinubu Ya Karrama ’Yan Wasan Super Eagles da Lambar MON, Ya Ba Su Kyautar Filaye da Gidaje a Abuja

Tinubu Ya Karrama ’Yan Wasan Super Eagles da Lambar MON, Ya Ba Su Kyautar Filaye da Gidaje a Abuja

  • Shugaba Bola Tinubu, a ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu, ya karbi tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Najeriya su 25 a fadar Aso Rock da ke Abuja
  • A wajen taron, shugaba Tinubu ya ba da lambar yabo ta 'Member of the Order of Niger (MON) ga daukacin tawagar, da kyautar gida da fili
  • Rashin nasarar Super Eagles ba laifin 'yan wasa kadai ba ne, har da na NFF da gwamnati, in ji Saminu Namunaye, mai sharhi kan wasanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya baiwa daukacin ‘yan kungiyar Super Eagles lambar karramawa ta kasa ta 'Member of the Order of Niger (MON).'

Kara karanta wannan

Ribadu: Bayanai sun fito bayan kus-kus da Hadimin Tinubu yayi da Sanatoci a Majalisa

Shugaban ya kuma ba wa kowannen su fili da gida a babban birnin tarayya Abuja don bajintar da ya yi a gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka kammala.

Shugaba Tinubu da wasu manyan jami’an gwamnatin sa ne suka tarbi Super Eagles
Shugaba Tinubu da wasu manyan jami’an gwamnatin sa ne suka tarbi Super Eagles a fadar Aso Rock. Hoto: @AfolabiBB
Asali: Twitter

Tawagar Super Eagles ta gana da Tinubu

Tawagar Super Eagles ta isa babban birnin tarayya Abuja, bayan da ta zo ta biyu a gasar bayan da ta sha kasa a hannun mai masaukin baki, Cote d'Ivoire.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin a karrama tawagar 'yan wasan 25 da ma'aikatan tawagar, sai da aka fara hada musu liyafar karin kumallo a Transcorp Hilton.

Manyan ‘yan wasa irin su Alex Iwobi, Ahmed Musa, Victor Osimhen, Ola Aina, Frank Onyeka, Calvin Bassey, Ademola Lookman, Kenneth Omeruo, Joe Aribo, da Williams Trost Ekong duk sun halarci liyafar .

Dolu Segun, hadimin Tinubu ne ya wallafa bidiyon karramawar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama mace da namiji turmi da tabarya a wajen bauta a jihar Arewa

A daina hantar 'yan wasan Super Eagles, har da laifin NFF - Namunaye

A zantawarsa da Legit Hausa, Saminu Namunaye daga jihar Bauchi ya ce tawagar Super Eagles ta yi kokari da har da yi nasarar zuwa wasan karshe a gasar wannan shekarar.

"Ni tun farko ma ban yi tunanin za su tsallake wasannin rukuni ba, saboda na lura akwai rashin hadin kai a tsakanin 'yan wasan, da wariya da hukumar NFF ta nuna a gasar."

A cewar Namunaye.

Gasar cin kofin nahiyar Afirka ba karamar gasa bace, tana bukatar jajurcewa da goyon baya daga 'yan kasa, amma 'yan Najeriya ne ke fatan kasar su ta fadi a gasar.

Ya ce:

"Ban ga dalilin da zai sa a zo ana hantarar 'yan wasan ba irin su Alex Iwobi, saboda kawai ba mu ci kofin ba, ai ba laifin Iwobi kadai ba ne, har da na gwamnati.
"Ana kusa da wasan zagayen karshe, mun ga yadda wasu 'yan wasan ke cewa ba a biya su alawus ba, ka ga a na gwamnati ba ta dauki matakin saka karsashi a zukatan 'yan wasan ba."

Kara karanta wannan

AFCON: Tinubu ya aika muhimmin sako ga Super Eagles bayan ta yi rashin nasara a wasan karshe

Namunaye ya kuma yi ikirarin cewa hukumar kwallon kafar Najeriya ta yi son kai a zaben 'yan wasan da za su buga kwallo, inda ya yi misali da ajiye Ahmed Musa da aka yi a benci.

Bayan wasan karshe, Tinubu ya jinjinawa tawagar Najeriya

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya jinjinawa tawagar Najeriya duk da cewa ba ta samu nasarar daga kofin AFCON ba.

A cewar shugaban kasar, kokarin da 'yan wasan sukayi har zuwa wasan karshe ya saka farin ciki a zukatan 'yan Najeriya, don haka wannan ma kadai ya wadatar

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel