Shugaba Tinubu Ya Gana da Tawagar Ƴan Kwallon Najeriya a Villa, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Gana da Tawagar Ƴan Kwallon Najeriya a Villa, Bayanai Sun Fito

  • Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin tawagar ƴan wasan Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja yau Talata
  • Wannan na zuwa ne awanni 48 bayan ƙungiyar kwallon ƙafa ta Najeriya Super Eagles ta yi rashin nasara a wasan karshe na gasar AFCON
  • Bayan doke su 2-1, Shugaba Tinubu ya yaba musu bisa yadda suka nuna jajircewa har suka taka matakin ƙarshe a gasar da aka kammala a ƙasar Côte d’Ivoire

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na ganawa yanzu haka da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Super Eagles a ɗakin taron da ke fadar Aso Villa a Abuja.

Tinubu ya karɓi bakuncin ƴan wasan kwallon ne sa'o'i 48 bayan sun sha kashi a wasan ƙarshe na gasar kofin nahiyar Afirka (AFCON) a hannun ƴan wasan Côte d’Ivoire.

Kara karanta wannan

Muhimmin dalilin 1 da ya sa Ivory Coast ta doke Najeriya a wasan ƙarshe na kofin AFCON

Tawagar yan wasan Najeriya da Tinubu.
Shugaba Tinubu Na Ganawa da Tawagar Yan Wasan Kwallon Najeriya Super Eagles a Villa Hoto: NGRPresident
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro cewa dukkan ƴan wasan Super Eagles da jami'an tawagar kwallon sun halarci wannan zama da ke gudana yanzu a fadar shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba, Shugaba Tinubu ya jinjinawa ƴan wasan Najeriya duk da rashin nasarar da suka yi ranar Lahadi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Me Tinubu ya faɗa bayan rashin nasarar Najeriya?

A wata sanarwa, shugaban ƙasar ya yabawa ƴan wasa, koci da sauran jami'ai bisa, "aiki tukuru da sadaukarwan da suka yi wanda ya sa suka kai matakin ƙarshe a gasar."

Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya da su kasance cikin farin ciki, yana mai jaddada cewa "mun samu gagarumar nasara a zukatan Afirka da ma duniya baki daya ta hanyar dagewa da jajircewarmu a fagen wasa."

"Kada wannan rashin nasara ta kashe mana guiwa, mu tashi mu ƙara dagewa da aiki tuƙuru. Mu ƴan ƙasa ɗaya ne da muka dunƙule karkashin tuta mai launin fari, kore da fari."

Kara karanta wannan

Najeriya vs Cote d'Ivoire: Shugaba Tinubu ba zai halarci wasan karshe na AFCON ba, bayanai sun fito

Ƴan wasan Najeriya sun yi rashin nasara da ci 2-1 a wasan karshe da suka fafata ƙasar Ivory Coast mai masaukin baƙi a Abidjan ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu.

Akpabio ya rantsar da Sanatoci 3 a Abuja

A wani rahoton kuma Majalisar dattawan Najeriya ta rantsar da sabbin sanatoci uku a zamanta na yau Talata, 13 ga watan Fabrairu, 2024 a birnin tarayya Abuja.

Sanata Godswill Akpabio ne ya jagoranci rantsar da sanatocin da misalin ƙarfe 11:41 na safe kuma daga bisani aka nuna musu wurin zamansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel