Sa'o'i Kadan Bayan Wani Abun Fashewa Ya Tashi, An Sake Samun Mummunar Gobara a Legas

Sa'o'i Kadan Bayan Wani Abun Fashewa Ya Tashi, An Sake Samun Mummunar Gobara a Legas

  • Wani sabon abu mara daɗi ya sake aukuwa a jihar Legas bayan wani abun fashewa ya tashi a unguwar Iju-Ishaga ta birnin
  • Wannan karon wata gobara ce ta tashi a wani gini mai hawa ɗaya na kasuwanci a kusa da ƙasan gada a 'Computer Village' da ke birnin Ikeja na jihar
  • Gobarar wacce ba a san musabbabin tashin ta ba dai, ta auku ne da safiyar ranar Laraba, 13 ga watan Fabrairun 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Wata gobara ta ƙone wani gini mai hawa ɗaya mai lamba 36, ​​a hanyar Awolowo, kusa da ƙasan gada, 'Computer Village', Ikeja, jihar Legas,

Gobarar wacce ta tashi da safiyar ranar Laraba, ta lalata wasu kayayyaki masu yawa na miliyoyin naira, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Mutane sun shiga fargaba sakamakon tashin abun fashewa a Legas, bidiyo ya bayyana

Gobara ta tashi a Legas
An sake samun tashin gobara a jihar Legas Hoto: Global Images Ukraine, Andrew Caballero-Reynolds
Asali: Getty Images

Sabon lamarin ya faru ne sa’o’i 12 bayan fashewar wata tankar iskar gas a daren ranar Talata a yankin Iju-Ishaga da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wani ganau, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9.45 na safiyar ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairun 2024.

Jami'ai sun ce ba a sami labarin asarar rai ba a sakamakon tashin gobarar.

An ga ƴan kasuwar da abin ya shafa suna ƙoƙarin ciro kayayyakinsu daga ginin da ya ƙone.

Me hukumomi suka ce kan gobarar?

Daraktar hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Misis Magaret Adeseye, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce, “An shawo kan lamarin.”

Adeyeye ta bayyana cewa:

"Wani gini mai hawa ɗaya na kasuwanci wanda ake amfani da shi a matsayin wurin ajiya, a 'Computer Village' ya ƙone daga ƙasa.
"Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba. Ya zuwa yanzu ba a samu asarar rai ba."

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi da sauran fitattun 'yan Najeriyan da suka rasu a hatsarin jirgin sama

Ga bidiyon da hukumar ta sanya kan gobarar a nan ƙasa:

Mummunar Gobara Ta Tashi a Jami'ar Jihar Yobe

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mummunar gobara ta tashi a ɗaƙin kwanan ɗalibai mata na jami'ar jihar Yobe.

Gobarar wacce ba a san musabbabin tashin ta ba ta ƙone ƙurmus wani rukunin ɗakunan ƙwana ɗalibai mao ɗauke da mutum 150.

Asali: Legit.ng

Online view pixel