Sarkin Musulmi da Sauran Fitattun 'Yan Najeriyan da Suka Rasu a Hatsarin Jirgin Sama

Sarkin Musulmi da Sauran Fitattun 'Yan Najeriyan da Suka Rasu a Hatsarin Jirgin Sama

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Hatsarin jirgin sama a Najeriya ya sha salwantar da rayukan manyan mutane waɗanda ake ji da su a ƙasar nan.

Daga cikin waɗanda hatsarin jirgin sama ya ritsa da su akwai, manyan ƴan kasuwa, sarakuna, gwamnoni da jami'an gwamnati.

'Yan Najeriya da suka rasu a hatsarin jirgin sama
Herbert Wigwe shi ne na baya-bayan nan cikin fitattun 'yan Najeriya da suka rasu a hatsarin jirgin sama Hoto: @SKUsman, @HerbertOWigwe
Asali: Twitter

Fitattun ƴan Najeriya da suka rasu a hatsarin jirgin sama

Jaridar Daily Trust ta tattaro wasu daga cikin fitattun ƴan Najeriya da suka rasa ransu a hatsarin jirgin sama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerinsu a nan ƙasa:

Herbert Wigwe

A ranar Juma'a, 9 ga watan Fabrairun 2023, Najeriya ta yi rashin haziƙi a fannin banki da hada-hadar kuɗi, kuma shugaban bankin Access, Herbert Wigwe, a wani hatsarin jirgin sama a Amurka.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Amarya ta hallaka mijinta a jihar Neja

Jaridar The Cable ta rahoto cewa, Wigwe dai yana tare da matarsa, ɗansa da wasu fasinjoji uku ciki har da tsohon shugaban kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya, Abimbola Ogunbanjo, lokacin da lamarin ya faru.

Patrick Yakowa

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Patrick Yakowa, ya mutu a wani jirgin sama mai saukar ungulu da ya faɗo kuma ya ƙone ƙurmus a dajin Okoroba da ke ƙaramar hukumar Nembe a jihar Bayelsa, jim kaɗan da tashinsa, cewar rahoton Sahara Reporters.

Patrick Yakowa ya riƙe muƙamin gwamnan jihar Kaduna daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2012.

Sultan Muhammadu Maccido Abubakar III

Shi ma Sarkin Musulmi na 19, Muhammadu Maccido Abubakar III, ya rasu a wani hatsarin jirgi da ya rutsa da shi a jirgin ADC Airlines a ranar 29 ga Oktoban 2006.

Hatsarin ya auku ne yayin da yake komawa Sokoto bayan ganawa da shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.

Kara karanta wannan

Okonjo-Iweala, Atiku sun yi martani bayan an tabbatar da mutuwar Herbert Wigwe, matarsa da dansa

Maccido ya rasu tare da ɗansa, Badamasi Maccido kuma an binne su a Sokoto.

Laftanar Janar Ibrahim Attahiru

Tsohon shugaban hukumar sojin ƙasa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, ya rasa ransa a cikin wani hatsarin jirgin sama da ya kashe jami’an soji 11 da ke cikinsa, a ranar 21 ga watan Mayun 2021.

Jirgin ya yi hatsari ne a kusa da filin jirgin sama na Kaduna a lokacin da jami’an sojin ke kan hanyarsu ta zuwa wajen bikin yaye sabbin sojojin da aka ɗauka, wanda aka shirya gudanarwa washe garin ranar.

Janar Andrew Owoye Azazi

Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Janar Andrew Owoye Azazi, wanda ya yi aiki a lokacin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, ya rasu hatsarin jirgin sama tare da marigayi Gwamna Yakowa a watan Disamban 2012.

Kafin rasuwarsa ya riƙe muƙamin babban hafsan tsaro na ƙasa (CDS) da shugaban hukumar sojin ƙasa (COAS).

Kara karanta wannan

Herbert Wigwe: Abubuwan sani 7 game da shugaban bankin Access da ya mutu a hatsarin jirgi

Atiku, Okonjo-Iweala Sun Yi Ta'aziyyar Herbert Wigwe

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da shugabar hukumar kasuwanci ta duniya, Ngozi Okonjo-Iweala, sun ƴi ta'aziyya kan rasuwar Herbert Wigwe.

Atiku da Okonjo-Iweala sun nuna takaicinsu kan rasuwar ɗan babban ɗan kasuwan wacce suka bayyyana a matsayin babban rashi ga iyalensa da ma Najeriya baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel