Mummunar Gobara Ta Tashi a Dakin Kwanan Dalibai Na Jami'ar Jihar Yobe, Gwamna Buni Ya Yi Martani

Mummunar Gobara Ta Tashi a Dakin Kwanan Dalibai Na Jami'ar Jihar Yobe, Gwamna Buni Ya Yi Martani

  • An shiga jimami bayan wata mummunar gobara ta tashi a ɗakin kwanan ɗalibai mata na jami'ar jihar Yobe
  • Gobarar wacce ba a san musabbabin tashin ta ba, ta yi sanadiyyar ƙona rukunin ɗakin kwanan ɗalibai mai ɗauke da ɗalibai kusan 150
  • A halin da ake ciki, Gwamna Mai Mala Buni na jihar ya nuna takaicinsa kan aukuwar lamarin inda ya umurxi hukumar SEMA ta kai agajin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - A ranar Talata an samu tashin gobara a ɗakin kwanan ɗalibai mata na jami’ar jihar Yobe.

Gobara wacce ta tashi da yammacin ranar, ta lalata katafaren ginin da ke ɗauke da ɗalibai mata kusan 150.

Kara karanta wannan

Dakarun EFCC sun kai samame ɗakunan ɗaliban fitacciyar jami'ar tarayya cikin dare, bayanai sun fito

Gobara ta tashi a jami'ar jihar Yobe
Gwamna Buni ya aike da sakon jaje kan gobarar da ta tashi a jami'ar jihar Yobe Hoto: Mai Mala Buni
Asali: Twitter

Ko da yake kawo yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba, wani ganau ya shaida wa jaridar Channels tv, cewa an kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban da ke babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me gwamnatin Yobe ta ce kan gobarar?

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya jajantawa mahukunta da ɗaliban jami’ar jihar Yobe kan gobarar da ta ƙona ɗaya daga cikin rukunin ɗakunan kwanan ɗalibai mata na jami'ar, cewar rahoton Daily Post.

Buni a wata sanarwa ta bakin mai magana da yawunsa, Mamman Mohammed ya bayyana gobarar a matsayin abin takaici da baƙin ciki.

Sai dai ya nuna jin daɗinsa da cewa ba a rasa rai ba a sakamakon tashin gobarar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Muna godiya da cewa duk da babbar gobara da ta ƙone ɗakin kwanan ɗaliban gabaɗaya, ba a samu asarar rai ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Amarya ta hallaka mijinta a jihar Neja

"An umurci hukumar SEMA da ta samar da abinci, sutura, da katifa yayin da gwamnati ke neman wani wurin kwana ga ɗaliban mata da gobarar ta shafa."

Gwamna Buni ya buƙaci ɗaliban da al’ummar jihar da su yi taka tsantsan tare da kaucewa ayyukan da za su iya haddasa gobara.

Ya ce gwamnati za ta duba musabbabin afkuwar gobarar don kiyaye sake afkuwar irin hakan a nan gaba.

Wani Abun Fashewa Ya Tashi a Legas

A wani labarin kuma, kun ji cewa mutane da dama sun shiga halin firgici bayan wani abun fashewa ya tashi a yankin Iju Ishaga na jihar Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa dai wani tulun iskar gas ne da ake dafa abinci da shi ya fashe, wanda hakan ya tayar da mummunar gobara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel