Jerin Kasashe Takwas da Suka Haramta Yin Bikin Ranar Masoya

Jerin Kasashe Takwas da Suka Haramta Yin Bikin Ranar Masoya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

An dade da sanin watan Fabrairu a matsayin watan soyayya kamar yadda ake bikin ranar masoya a duk shekara a ranar 14 ga wannan wata.

A ƙasashe da yawa, mutane suna yin wannan bikin don nunawa masoyansu yadda suke kaunarsu ta hanyar basu kyautar kyawawan furanni da kyaututtuka.

A gefe guda kuma, yawancin ƙasashen Gabas sun zaɓi kada su yi bikin ranar soyayya saboda bambancin addini, The Nation ta ruwaito.

Jerin kasashe takwas da suka haramta yin bikin ranar masoya.
Jerin kasashe takwas da suka haramta yin bikin ranar masoya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ga jerin kasashen da ba sa bikin ranar masoya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Uzbekistan

A shekarar 2012 ne gwamnatin Uzbekista ta saka wata doka ta cikin gida da ta hana bikin ranar masoya kamar yadda ma'aikatar wayar da kai ta kasar ta sanar.

Kara karanta wannan

Hanya 1 tak da jami'an tsaron Najeriya suka dauka don kama 'yan ta'adda cikin sauki

Maimakon bikin ranar masoya, mutane a Uzbekistan suna bikin ranar haihuwar jarumin ƙasarsu, Babur, Sarkin Mughal.

2. Iran

Hukumomin Iran sun hana bukukuwan ranar masoya, sun kira bikin a matsayin "al'adar yammacin Turai" tare da barazanar hukunta shaguna da gidajen cin abinci idan suka sayar da kyaututtuka da sunan bikin ranar.

Duk da haka, an ba da rahoton cewa an kama hayar gidajen abinci da yawa a Tehran kuma an ga shaguna da yawa suna sayar da 'yar tsana da cakulan don murnar ranar.

3. Malaysia

Tun shekara ta 2005, sashen ci gaban Musulunci na Malaysia ya hana gudanar da bukukuwan ranar masoya akan hujjar ana tu'ammali da barasa da kuma kaiwa ga zubar da ciki.

Har ma akwai gangamin ranar kin jinin bikin ranar da aka ware na shekara-shekara don ƙarfafa ra'ayin illar gudanar da wannan biki.

4. Indonesia

Babu wata doka da ta haramta bikin ranar masoya a Indonesia

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta tashi a ofishin 'yan sandan Kano

To sai dai kuma a wasu yankunan kasar kamar Surabaya da Makassar inda mutane ke da yawan Musulmi masu tsatsauran ra'ayi, ana amfani da kananan matakan hana bukin.

5. Saudiyya

A Saudiyya, jami'ai sun sanya dokar haramta gudanar da bikin ranar masoya. An haramta sayar da fulawa, jajayen kayayyaki da katunan soyayya kafin ranar 14 ga Fabrairu.

Lamarin ya haifar da samar da bakar kasuwa na sayar da kayayyakin ranar soyayyar.

6. Pakistan

Pakistan wata kasa ce da ke da ra'ayoyi daban-daban game da ranar soyayya. Pakistan ta sha fama da tarzoma da dama dangane da bikin ranar masoyan.

A shekarar 2014, jami'o'i biyu a Peshawar da Pakistan sun yi arangama da akidar juna kan bikin ranar soyayya a idon shari'ar Musulunci.

7. Indiya

Sakamakon juyin juya hali don cin gashin kanta daga daular Burtaniya a 1947, gwamnatin Indiya ta ki amfani da dabi'u da al'adun Yammacin Turai.

A cikin 2015, shugaban jam'iyya Chandra Prakash Kaushik ya shaida wa jaridar Times of India cewa:

Kara karanta wannan

Dilolin wiwi a Morocco sun kaurayewa siyan kaya daga kasar Isra'ila saboda gallazawa Gaza

"Ba ma adawa da soyayya, amma idan namiji da mace suna soyayya to dole ne su yi aure."

8. Rasha

A zahirance, Rasha tana bikin ranar masoya, amma ya sha bamban da bikin na gama-gari.

Maimakon yin bikin ranar soyayya, Rasha ta zaɓi yin bikin soyayya ga matansu, suna ba da kyauta ga mata a duk faɗin duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel