'Yan Najeriya Sun Shiga Jimamin Rashin da Super Eagles Ta Yi a Wasan AFCON 2023, GA Martaninsu

'Yan Najeriya Sun Shiga Jimamin Rashin da Super Eagles Ta Yi a Wasan AFCON 2023, GA Martaninsu

  • ‘Yan Najeriya sun bayyana koke da jimamin rashin da Super Eagles ta yi a wasan karshe na kofin zakarun Afrika da aka daddale
  • An ruwaito cewa, Kasar Ivory Coast ce ta yi nasara a wasan da aka gudanar a yau Lahadi 11 ga watan Faburairun 2024
  • Ya zuwa yanzu, ‘yan Najeriya na ci gaba da bayyana yadda suka ji kan wannan babban rashi da suka tafka a daren yau

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Twitter - Bayan kammala wasan karshe na AFCON 2023, ‘yan Najeriya da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan rashin da Super Eagles ta yi a wasan karshe.

Kara karanta wannan

AFCON: Mourinho ya fadi kasar da ya ke so ta lashe gasar, ya tura sako ga abokinsa, Peseiro

Idan baku manta ba, an gwabza wasa tsakanin Najeriya da Ivory Coast, inda aka durawa Najeriya kwallaye biyu a raga, Ivory Coast kuma aka sha ta daya.

Bayan haka ne kafar sada zumunta, musamman ta dauki dumi da cece-kuce kan wannan nasara da kasa mai masaukin baki ta yi.

An daura laifin faduwar Super Eagles kan Tinubu
Tinubu ne ya ja Super Eagles ta fadi, 'yan Najeriya | Hoto: NGSuperEagles
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro muku kadan daga abin da mutane ke cewa kan wannan faduwa na Najeriya da kuma nasara na Ivory Coast.

Martanin ‘yan Najeriya a Twitter

@JaypeeGeneral:

“Ban ji dadi ba, amma ya wuce.Tinubu ne ya jawo mana!”

@omoba4rmdahbloc:

“Tinubu da Iwobi ne suka jawo mana wannan matsala.”

@Sarki_sultan:

“Tinubu ya hasaso mana wannan faduwa.”

@Ibrahim_mikiya:

“Na taya ku murna Super Eagle. Akalla kun saka mu alfahari.”

@WaruiJohn2:

“Najeriya ba za ta yi nasarar komai ba sai da firaneti... mun gargade ku dama...Mun gode Allah Cote D’Ivoire ta lallasa taron yuyuyu.”

Kara karanta wannan

An ji kunya: Matasa masu karfi a jika sun kashe zuciyarsu, sun sace fanka a masallaci

@Kayloaded1:

“Ku kori wancan shirmen kocin naku. Ta yaya za ku zo har wasan karshe amma ku gaza. Wannan lamari da zafi yake, babu abin da suka yi a wasan.”

@JaypeeGeneral:

“Laifin Bola Tinubu nake gani daga wannan sakamakon.”

Kashim ya je Abdijan shajja'a 'yan Najeriya

A tun farko, Kashim Shettima ya tashi daga fadar shugaban kasa domin nuna magoya bayan Najeriya wajen shajja’a Super Eagles ta Najeriya a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) na 2023 da Cote d'Ivoire mai masaukin baki a Abidjan.

A baya dai an ruwaito cewa shugaba Tinubu na shirin zuwa kallon wasan Najeriya da makwabciyarta Cote d'Ivoire a kasar ta Afrika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel