An Shiga Rudani Kan Batun Mutuwar Babban Basarake a Najeriya, An Fadi Gaskiyar Abin da Ya Same Shi

An Shiga Rudani Kan Batun Mutuwar Babban Basarake a Najeriya, An Fadi Gaskiyar Abin da Ya Same Shi

  • Fadar mai martaba Asagba na Asaba ta fito ta yi magana kan batun mutuwar basaraken da aka yi ta yaɗawa
  • Fadar ta bayyana cewa basaraken wanda yake dab da cika shekara 100 a duniya yana nan a raye da ransa bai mutu
  • Sakataren fadar wanda ya musanta batun mutiwar basaraken, ya bayyana cewa mai martaba sarkin an kwantar da shi ne akwai a asibiti

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - An samu tashin hankali game da mutuwar Asagba na Asaba, Obi Chike Edozien.

Sai dai fadar a ranar Alhamis, ta ce basaraken gargajiyar yana kwance a asibiti ne kawai bai mutu ba, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Asagba na Asaba bai mutu ba
An musanta batun mutuwar Asagba na Asaba mai martaba Obi Chike Edozien Hoto: @edevbieofficial, @BasafGhali
Asali: Twitter

Sakataren fadar, Ogbueshi Ndili ya bayyana haka lokacin da aka tuntuɓe shi ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilan Tarayya ta bayyana Mataki mai kyau da ta ɗauka domin share hawayen ƴan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mai Martaba Sarki yana kwance a asibiti ne kawai. Idan mutuwa ta riske shi, za mu sanar."

Hakazalika, da aka tuntubi ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Oshimili ta Kudu a majalisar dokokin jihar, Bridget Anyafulu, kan wannan jita-jitar, sai ya kada baki ya ce:

“Ban san komai ba game da hakan.”

An yi ta yaɗa jita-jita da sanyin safiyar ranar Alhamis cewa, sarkin mai shekara 99 wanda zai cika shekara 100 a ranar 28 ga watan Yulin wannan shekara ya rasu, lamarin da ya haifar da fargaba a Asaba babban birnin jihar.

Jigon APC ya yanke jiki ya mutu

Wani jigon jam'iyyar APC kuma tsohon ɗan majalisar wakjilai, wanda ya wakilci mazabar Ika ta jihar Delta a majalisar tarayya, Cairo Ojougboh, ya yi bankwana da duniya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da mummunar gobara ta ɓarke a sakateriyar ƙaramar hukuma, bayanai sun fito

Ojougboh, wanda ya shahara saboda rashin tsoron fitowa ya yi magana ya rasu ne a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, yayin da yake kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu a gasar AFCON 2023.

Mataimakin Bursar Ya Rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin Bursar na jami’ar jihar Kwara, Alhaji Ayuba Abdullahi, ya rasu a daren Laraba.

Marigayin ya rasu ne a lokacin da yake kallon wasan kusa da na ƙarshe tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel