Mataimakin Bursar Na Jami’ar Kwara Ya Rasu Yana Kallon Wasan Super Eagles da Afrika Ta Kudu

Mataimakin Bursar Na Jami’ar Kwara Ya Rasu Yana Kallon Wasan Super Eagles da Afrika Ta Kudu

  • Alhaji Ayuba Abdullahi, mataimakin Bursar na jami'ar jihar Kwara ya kwanta dama a yayin da yake kallon kwallon Najeriya da Afrika ta Kudu
  • An ruwaito cewa hawan jinin Abdullahi ne ya tashi ana daf da kammala buga wasan, inda ya yanke jiki ya fadi aka garzaya da shi asibiti
  • Sai dai ba a karasa da shi asibitin ba ya ce "ga garin ku", kamar yadda wata majiya ta tabbatar da faruwar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kwara - Mataimakin Bursar na jami’ar jihar Kwara, Alhaji Ayuba Abdullahi, ya rasu a daren Laraba a lokacin da yake kallon wasan kusa da na karshe tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu.

Kara karanta wannan

Babban jigon APC ya yanke jiki ya mutu yayin da ya ke kallon wasan Najeriya

Najeriya ta samu nasara a karawar da ta yi da Afrika ta Kudu da ci 4-2 a bugun fenariti bayan da aka tashi wasa da kuma karin lokaci da ci 1-1.

Alla ya karbi rayuwar Alahaji Ayuba, Bursar na jami'ar Kwara
Alla ya karbi rayuwar Alahaji Ayuba, Bursar na jami'ar Kwara yana kallon wasan Eagles. Hoto: @KwasuOfficial
Asali: Twitter

Yadda mataimakin Bursar ya rasu

Majiyoyin da ke kusa da marigayin amma wadanda suka nemi a sakaya sunansu sun ce Abdullahi ya je gidan kallon kwallo da ke yankin Sango lokacin da jikinsa ya tashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Punch ta ruwaito daya daga cikin majiyoyin na cewa:

“Mataimakin Bursar ya kalli wasan Najeriya da Afirka ta Kudu tun daga farko har zuwa karshen karin lokacin, har lokacin da aka yi bugun fanareti.
“Ya yi korafin cewa yana jin jiri, don haka ya ce yana bukatar ya koma gida ya huta ba tare da sanin cewa jininsa ne ya hau ba.

Jami'ar Kwara ta magantu kan mutuwar Abdullahi

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ku yi hakuri da Tinubu, jigon APC ya roki 'yan Najeriya

Ya kara da cewa:

“Da ya dawo gida, sai ya yanke jiki ya fadi, aka garzaya da shi wani asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin amma kafin a kai shi ya rasu.
"An yi jana'izarsa a safiyar ranar Alhamis kamar yadda addinin Musulunci ya tanada."

Daraktar yada labarai ta jami’ar, Dr Saedat Aliyu, ta tabbatar da rasuwar Abdullahi.

Aliyu, ta bayyana cewa hukumar gudanarwar jami'ar ba ta da cikakkiyar masaniya har yanzu akan musabbabin mutuwar Abdullahi ba.

Dokta Cairo Ojougboh, ya mutu yana kallon wasan Eagles

A wani labarin, wani tsohon dan majalisar tarayya a jihar Delta, Dokta Cairo Ojougboh, ya mutu a lokacin da yake kallon wasan Eagles.

Wata majiya da ke kusa da dan siyasar ta ce:

“Cairo Ojougboh, wanda likita ne ya mutu yana kallon wasan Najeriya da Afirka ta Kudu.
“Al’amarin ya faru ne a lokacin da za a buga wa Najeriya fanareti. Dr Ojougboh ya yi kururuwa kuma ya fadi saboda tsananin bugun zuciya lokacin aka zura kwallo a ragar Najeriya.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel