Tashin Hankali Yayin da Mummunar Gobara Ta Ɓarke a Sakateriyar Karamar Hukuma, Bayanai Sun Fito

Tashin Hankali Yayin da Mummunar Gobara Ta Ɓarke a Sakateriyar Karamar Hukuma, Bayanai Sun Fito

  • Gobara ta tashi a sakateriyar ƙaramar hukuma ɗaya a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya
  • Shugaban hukumar kwana-kwana na jihar, Martin Agbili, ya ce tuni suka tura jami'ai kuma sun kashe wutar a jiya Laraba da yammaci
  • Wani mazaunin yankin ya ce zuwan jami'an kashe wuta a kan lokaci ya taimaka wajen daƙile wutar daga yin mummunar ɓarna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Rahotanni sun bayyana cewa wuta ta kama rigi-rigi a sakateriyar ƙaramar hukumar Dunukofia da ke jihar Anambra.

Gobarar wacce ta afku da yammacin ranar Larabar da ta gabata, an ce ta taso ne daga wata gobarar daji da ke kusa da sakatariyar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An shiga rudani kan batun mutuwar babban basarake a Najeriya, an fadi gaskiyar abin da ya same shi

Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo.
Gobara Ta Barke a Hedkwatar Karamar Hukuma Guda a Jihar Anambra Hoto: Charles Soludo
Asali: Facebook

Wani mazaunin unguwar, Mista Frank Okolie, ya bayyana cewa gobarar ta dauki tsawon sa'o'i tana ci a gidan gwamnatin ƙaramar hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, ba don ɗaukin gaggawa da jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Anambra suka kai ba, da wutar ta ƙone kadarori masu ɗumbin yawa.

Shugaban hukumar kashe gobara na jihar Anambra, Injiniya Martin Agbili, wanda ya tabbatar da faruwar ibtila'in, ya ce:

"Da misalin karfe 6:53 na yammacin ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, 2024, muka samu rahoton ɓarkewar wuta a garin Dunukofia."

Wace ɓarna gobarar ta yi?

Ya ce nan take hukumar ta tura motar kashe wuta da jami'ai zuwa wurin, yana mai ƙara da cewa wutar ta kama ne sakamakon ƙona daji da ke kusa.

Mista Agbili ya ci gaba da cewa, yayin aikin kashe gobara sun yi nasarar shawo kan wutar da ke yaɗuwa tare da hana ta lalata abubuwa da dama a sakatariyar karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame malamin addini da matarsa saboda babban laifi 1 da suka aikata

A ruwayar Channels tv, ya ce:

"Mun janye daga wajen da gobarar ta tashi da misalin karfe 8:30 na dare bayan mun yi nasarar daƙile wutar tare da kwantar da hankula.
"Yana da mahimmanci mu share duk ciyayi da ke kewaye da muhallinmu, musamman a wannan lokaci na rani da sanyi. Wuta tana kisa mma za mu iya kiyaye ta."

Sojoji sun samu nasara a jihar Katsina

A wani rahoton kuma Dakarun rundunar sojin Najeriya sun kai samame mafakar ƴan bindiga a Katsina, sun ceto mata 18 da aka yi garkuwa da su.

Kwamandan rundunar Birgade ta 17 ya ce sojojin sun yi gumurzu da ƴan ta'addan kafin su samu wannan nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel