Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki Cikin Makonni 2

Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki Cikin Makonni 2

  • Kungiyar malam jami'a ta kasa (ASUU) ta yi barazanar tsunduma yajin aiki cikin makonni biyu idan gwamnati ta gaza sauraronta
  • Shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana lamarin ga manema labarai a ranar Talata a jami'ar Abuja
  • Farfesa Emmanuel Osodeke ya kuma lissafa abubuwa guda tara da kungiyar ke neman gwamantin Bola Tinubu ta sauraresu a kai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ta ba gwamnatin shugaba Bola Tinubu wa'adin makonni biyu domin biya mata bukatun ta ko ta tsunduma yajin aiki.

A jiya Talata ne shugaba kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana wa manema labarai matakin da suka dauka.

Kara karanta wannan

"Akwai yiwuwar gwamnatin Tinubu ta kara kasafin 2024 domin gyara albashin ma'aikata," IMF

ASUU strike
Kungiyar ASUU za ta shiga yajijn aiki saboda gazawar gwamnatin Tinubu. Hoto: @Flexyeffiong, @KAFTAN_TV
Asali: Twitter

ASUU da gwamnatin Bola Tinubu

Rahoton jaridar Punch ya ruwaito shugaban ASUU yana cewa sun ba gwamantin Bola Tinubu wadataccen lokaci da za ta magance matsalolinsu amma ta gagara taɓuka komai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau shugaban kungiyar malaman ya ce majalisar zartarwar ASUU za ta zauna domin kara kallon lamarin.

A cewarsa majalisar zartarwar ta lura da cewa gwamnatin ta nuna halin ko in kula kan matsalolin kungiyar saboda haka dole su dauki mataki, rahoton Business Day.

Manyan bukatun kungiyar ASUU guda 9

1. Farkon abin da ASUU ta zargi gwamnatin Tinubu da shi shi ne rashin bada kofa domin cigaba da tattaunawa kan yarjejeniyar da suka yi da gwamnati a 2009.

Yarjejeniyar za ta bada dama wurin samun walwala ne ga malaman jami'a domin yin aiki cikin tsari.

2. Abu na biyu shi ne rusa tsarin majalisun gudanar da jami'o'i da shugaba Tinubu ya yi a watan Yunin 2023.

Kara karanta wannan

"Wannan ai sata ce," NLC ta magantu kan karin kudin wutar lantari a Kogi

Kungiyar ta ce rusa majalisun ya saɓa dokar kasa kuma ya haifar da giɓi babba a aikin jami'a a Najeriya.

3. Abu na gaba da kungiyar ASUU ta zargi gwamnatin a kai shi ne cigaba da biyan malaman jami'a albashi ta manhajar IPPIS.

Duk da cewa Bola Tinubu ya ce an cire malaman jami'o'i a tsarin tun watan Disambar bara amma kungiyar ta ce babu abin da ya canja.

4. Lamarin na hudu da zai iya jefa kungiyar yajin aiki shi ne fitar da sabon tsarin karatun jami'a a Najeriya.

Kungiyar ta yi watsi da sabon tsarin da gwamnati ta fitar na karatun jami'a duk da cewa gwamnatin na kokarin tilasta aiki da shi.

5. Yawaitar jami'o'in gwamnati a Najeriya shi ne abu na biyar da kungiyar ta koka ga gwamnatin Bola Tinubu.

ASUU ta ce maimakon inganta jami'o'in da ake dasu gwamantin ta dukufa wurin samar da sababbin jami'o'in da ba za ta iya daukan nauyinsu yadda ya kamata ba.

Kara karanta wannan

Wahalar Rayuwa: Ka da a Karaya da Mulkin Bola Tinubu, Jigon APC Ya Lallabi Mutane

6. Abu na shida da ake dambarwa a kai shi ne cigaba da ɗaukan dawainiyar jami'o'i yadda ya kamata.

Kungiyar ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da kokarin karkatar da kudaden da hukumar TETFund ke amfani da su wajen raya jami'o'i zuwa harkokin lamunin dalibai.

7. Korar ma'aikatan jami'a ba bisa ka'ida ba shi ne abu na bakwai da kungiyar ASUU ta ke kalubalantar gwamantin Tinubu.

Kungiyar ta ce tana da rahotanni a kan yadda ake wulakanta jami'anta a jami'ar Lagos da jami'ar Kogi da jami'ar fasaha da ke Owerri.

8. Abu na takwas da kungiyar ASUU ta koka shi ne yadda gwamnatin to tsohe kunnuwa kan alawus da ya kamata ta biya ta.

Gwamnatin ta gaza saka kudin alawus din da kungiyar ke binta a cikin kasafin kudin shekarar 2023.

9. A karshe kungiyar ta koka kan yadda lamura suka tabarbare a Najeriya da yadda talakawa ke kara shiga kuncin rayuwa.

Kara karanta wannan

GCON: Tinubu ya ba Sarkin yarbawa lambar karramawa ta 2 mafi girma a Najeriya

A cewar kungiyar ASUU, dole gwamantin Bola Tinubu ta nemo mafita domin saukaka rayuwar al'ummar Najeriya.

Gwamnatin tarayya za ta biya ma'aikatan jami'a bashi

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta ce akwai yiwuwar ta biya ma'aikatan ilimi na SSANU da NASU rabin albashisu da suke bin ta tun 2022.

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana hakan, inda ya ce su na kokarin biyan ma'aikatan domin sama musu saukin gudanar da ayyuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel