NYSC Ta Tura Matasa ’Yan Bautar Kasa 10 Zuwa Kasar Indiya da Sunan Yiwa Najeriya Aiki

NYSC Ta Tura Matasa ’Yan Bautar Kasa 10 Zuwa Kasar Indiya da Sunan Yiwa Najeriya Aiki

  • Matasa ‘yan bautar kasa na NYSC 10 ne suka shilla kasar Indiya a ranar Lahadi, 14 ga watan Janairu da izinin gwamnatin Najeriya
  • Shugaban NYSC na kasa, Birgediya Janar YD Ahmed ya bukaci matasa da su kasance masu da’a kamar yadda hukumar ta tanada
  • Ahmed ya ce an yi hakan ne a shirin bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai na kasa Indiya mai kawance da Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Hukumar Kula da Matasa masu yiwa Kasa Hidima (NYSC) ta sanar da cewa ta tura wasu matasa 10 zuwa kasar Indiya domin halartar wani shirin musayar matasa da kungiyar Kadet Corps ta Indiya ta shirya.

A cewar sanarwar da NYSC ta yada Twitter, matasan ‘yan bautar kasa sun tashi zuwa Indiya a ranar Lahadi, 14 ga Janairu.

Kara karanta wannan

"Kada ku tsinewa shugabanninmu": Sarkin Musulmi ya aika muhimmin sako ga yan Najeriya

Ana gudanar da shiri irin wannan a kowace shekara don tunawa da zagayowar ranar samun 'yancin kai na Indiya kuma akan samu mahalarta daga Turai, Asiya, Afirka da sauran nahiyoyi.

'Yan Najeriya za su tafi Indiya bautar kasa
'Yan Najeriya sun tafi bautar kasa Indiya | Hoto: @officialnyscng
Asali: Twitter

Abin da NYSC tace game da tafiyar

Babban Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed, ya nuna jin dadinsa ga gayyatar da aka yiwa Najeriya don halartar wannan biki mai tarihi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya bayyana cewa, gayyatar, kasancewar ta biyu, wata dama ce ga NYSC ta nunawa duniya kwazon matasan Najeriya, tare da baiwa mahalartan damar fahimtar kamanceceniya da zamantakewar tattalin arzikin da ke tsakanin kasashen biyu.

Ahmed ya bayyana hakan ne a taron tattaunawa da manema labarai a ofishin babban kwamishinan Indiya da ke ofishin jakadancin kasar a Abuja.

Ya taya matasan murna bisa zabansu da aka yi zuwa wajen taron, ya kuma umurce su da su kasance masu da’a daidai da tsari da kuma tanadin dokar NYSC.

Kara karanta wannan

Atiku ya faɗi shirinsa na gaba kan Tinubu da APC bayan gwamnoni 4 sun yi nasara a kotun ƙoli

‘Yar Najeriya ta yi tarihi a Indiya

Wata ‘yar Najeriya ta shiga cikin littafin tarihi a Kasar India bayan da ta zo ta daya a wasanni da aka yi a Jami’ar Amity da ke Garin Haryana a Kasar India.

Wannan ‘Yar Najeriya tana da shekaru 17 ne a duniya, sannan kuma tana aji biyu na karatu. The Nation ta rahoto cewa ba tun yau wannan yarinya mai suna Esther Ruby Daniel ta fara samun nasara a wasannin Jami’ar ba, tun tana aji daya ta saba cin wasanni.

Esther Daniel ta samu kyautar zinari a Gasar wasanni na daliban shari’a a watan ta na farko a makarantar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel