‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari Jihar Arewa, Sun Sheke Mutum 6 da Sace Mata 20

‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari Jihar Arewa, Sun Sheke Mutum 6 da Sace Mata 20

  • Tsagerun 'yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun farmaki bayin Allah a yankin karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja
  • Maharan sun hallaka mutane shida da suka hada da maza hudu da mata biyu, sannan suka yi awon gaba da wasu mata 20
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago ya bayyana cewa an samu karin matakan tsaro a Neja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Niger - An rahoto cewa 'yan bindiga sun hallaka manoma shida yayin da suka yi garkuwa da akalla mata 20, a mararrabar Maganda da ke hanyar Allawa-Pandogari a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

'Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Neja
‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari Jihar Arewa, Sun Kashe Mutum 6 da Sace Mata 20 Hoto: Gov. Mohammed Umaru Bago
Asali: Facebook

Yadda 'yan bindiga suka sheke mutum shida a jihar Neja

Wani mazaunin yankin, Salihu Adamu, wanda ya bayyana cewa mutanen da aka kashe sun kasance maza hudu da mata biyu, ya ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi bayanin cewa wadanda abin ya ritsa da su suna a hanyarsu ta komawa garin Allawa a karamin hukumar Shiroro ne lokacin da abin ya faru, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sun fito ne daga garin Pandogari da ke karamar hukumar Rafi lokacin da 'yan bindigan suka budewa motocinsu wuta.

Adamu ya ce:

"'Yan bindigan sun dasa abubuwan fashewa a kan hanya. Kuma da ganin ayarin motocin da suka nufi Allawa daga Pandogari, sai su (’yan bindiga) suka bude wa motocin wuta.
"A nan ne suka kashe mutane shida, wadanda suka hada da maza hudu da mata biyu. Mutane 3 ne suka samu raunuka, sannan an kona wasu manyan motoci guda biyu makil da kayan abinci."

Kara karanta wannan

Ina sukar biyan da kudin fansa a baya, sai da aka sace ni na gane, tsohon shugaban DSS ya magantu

Manomanmu sun koma gonakinsu saboda tsaro ya inganta - Bago

A halin da ake ciki, Gwamna Mohammed Umaru Bago, ya bayyana a ranar Litinin, cewa an samu karin matakan tsaro a jihar Neja, inda ya ce tuni manoma suka koma gonakinsu.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga zanga-zangar matsin rayuwa da aka gudanar a garin Minna, babban birnin jihar, Sahara Reporters ta ruwaito.

Bago ya ce:

“Akan matsalar rashin tsaro, gaskiya zan iya cewa mun lura da ;karuwar matakan tsaro a Jihar Neja. Manomanmu sun koma gonakinsu.”

Gwamna Uba Sani ya fadi hanyar samun tsaro

A wani labarin, gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa talauci da rashin aikin yi ne suka haddasa matsalolin tsaro na ‘yan fashi da sace-sacen jama’a a yankin Arewa maso Yammacin kasar.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa hanya mafi dacewa da za a bi wajen shawo kan matsalar ita ce wanzar da shugabanci na gari, jaridar Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel