Zanga-Zanga Ta Barke a Sansanin NYSC na Abuja Bayan Soja Ya Lakadawa Dan NYSC Duka

Zanga-Zanga Ta Barke a Sansanin NYSC na Abuja Bayan Soja Ya Lakadawa Dan NYSC Duka

  • Da safiyar yau ce aka samu hatsaniya inda kwamandan sansanin horas da masu bautar kasa ya lakadawa mai bautar kasa duka
  • Lamarin ya faru ne a sansanin horaswar da ke birnin Abuja inda ake zargin an fasa wa matashin wayar salula da kuma agogon hannu
  • A karshe, daraktar sansanin ta tabbatar da cewa an sallami kwamandan inda ta ce za a biya matashin asarar da aka masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An samu hatsaniya a sansanin horas da matasa masu yi wa kasa hidima a birnin Abuja.

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Laraba 13 ga watan Disamba da misalin karfe 9:30 inda wani soja ya lakadawa wani dan bautar kasa duka.

Kara karanta wannan

Cibiyar samar da wutan lantarkin Najeriya ta sake durkushewa a karo na uku

An samu hatsaniya bayan soja ya lakadawa dan NYSC duka a Abuja
Zanga-Zanga ta barke a sansanin NYSC na Abuja bayan soja ya yi wa matashi duka. Hoto: NYSC, Abuja.
Asali: Facebook

Mene dalilin rikicin a sansanin NYSC na Abuja?

Yayin dukan, sojan ya fasa wa matashin wayar salula da kuma agogon hannu mai tsada yayin da matasan su ka fito zanga-zanga don nema wa dan uwansu hakki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hausa Legit ta samu wani faifan bidiyo inda matasan su ka cika harabar daraktar sansanin don bin kadu.

Wani daga cikin masu karbar horaswar a sansanin da ya bukaci a boye sunansa ya bayyana wa Hausa Legit yadda abin ya kasance.

Ya ce:

"An bukaci mu shiga lakca, wasu sun tsaya a wurin siyar da abinci sai mu ka ji ana ihu ashe sojoji ne su ke korar masu bautar kasa.
"Wani soja ya doki wani dan bautar kasa wanda har ya fasa masu wayar salula da kuma agogon hannu mai tsada.
"Daraktar sansanin ta yi alkawarin za su dauki mataki inda ta ce an kori kwamanadan kuma za a kawo wani."

Kara karanta wannan

Tinubu ya gargadi sojojin Najeriya: "Kar ku kuskura ku kara jefa bam kan fararen hula"

Wane mataki aka dauka a sansanin?

Majiyar ta kara da cewa an bukaci matashin ya bayyana abin da aka fasa masa inda hukumomi su ka yi alkawarin biyanshi duk abin da ya yi asara.

Majiyar ta tababar cewa an karo sojoji da jami'an SARS don gudun rashin hankali a sansanin.

A yanzu haka an kawo sabon kwamanda a sansanin mai suna Major O. Emineokum wanda ya ii jawabi ga daruruwan matasan a sansanin.

Gwamna ya sanar da karin alawus ga matasan NYSC

A wani labarin, Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya bayyana biyan dubu 10 ko wace wata ga matasa masu bautar kasa.

Gwamna ya ce hakan zai tallafa wurin rage radadin cire tallafin mai da ake fama da shi a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel