Gwamnatin tarayya ta gano ma'adanin 'Nickel' a arewacin Najeriya
Labarin da muke samu na nuni da cewa gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ta jagoranci wani bincike da yayi sanadiyyar gano wani muhimmin ma'adani na 'Nickel' a kudancin jihar Kaduna dake a arewacin Najeriya.
Mun dai samu labarin cewa shi dai wannan ma'adani yana da matukar tasiri da kuma alfanu a rayuwar dan adam musamman ma a wannan zamanin da muke ciki.
KU KARANTA: Ahir din ku da yiwa Buhari fatar mutuwa - Wani Fasto
Legit.ng ta samu dai cewa tuni har gwamnatin tarayyar ta hannun hukumar kula da ma'adanan kasa ta fara gayyato manyan kamfaoni da kuma yan kasuwa a dukkan fadin duniya da su zo don su hako ma'adanin su siya.
Mun dai samu labarin cewa wannan ma'adanin an gano shi ne da yawan gasken da ya kai fadin kasa na ma'aunin kilomita 20 a kauyen Dagoma dake a kudancin jihar ta Kaduna.
Haka ma dai binciken mu ya gano kadan daga cikin abun da ake yi da ma'adanin sun hada da wayar salula, kayayyakin asibiti, kayayyakin noma da wajen kera motoci da kuma kayan gine-gine da dai sauran su.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng