Koya Min Yadda Ake Komawa Majalisar Dattawa Ba Tare Da Takarar Zaben Fidda Gwani Ba, Okorocha Ya Zolayi Lawan

Koya Min Yadda Ake Komawa Majalisar Dattawa Ba Tare Da Takarar Zaben Fidda Gwani Ba, Okorocha Ya Zolayi Lawan

  • Sanata Rochas Okorocha ya yi shagube ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan kan komawarsa majalisar dattawa ta 10
  • Tsohon gwamnan jihar Imo ya ce har yanzu bai san ya aka yi Lawan wanda ya yi takarar shugaban kasa ya samu damar komawa majalisar dattawa ba
  • Okorocha ya ce zai zo daukar darasi a wajen shugaban majalisar dattawan mai barin gado

Abuja - Sanata mai wakiltan Imo ta yamma, Rochas Okorocha, ya bukaci shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da ya koya masa yadda ake komawa majalisar dattawan ba tare da mutum ya yi zaben fidda gwani ba.

Tsohon gwamnan na jihar Imo ya fadi hakan ne yayin zaman bankwana na majalisar dattawa ta tara a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Lawan Ahmad da Rochas Okorocha
Koya Min Yadda Ake Komawa Majalisar Dattawa Ba Tare Da Takarar Zaben Fidda Gwani Ba, Okorocha Ya Caccaki Lawan Hoto: Senator Dr Ahmad Ibrahim Lawan
Asali: Facebook

Lawan zai kasance cikin majalisar dattawa ta 10 bayan ya yi yunkurin zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa: Rahoto Ya Nuna Yan Majalisa Na Iya Siyar Da Kuri’unsu $5,000, $10,000 Ko Fiye da Haka

Daga Lawan da Okorocha sun yi takarar zaben fidda gwani na APC tare amma suka sha kaye a hannun shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shiga zaben fidda gwanin da shugaban majalisar dattawan ya yi zai hana shi takarar tikitin sanata mai wakiltan Yobe ta arewa a jam'iyyar APC, kamar yadda dokar zabe ta tanadar.

An ayyana Bashir Machina a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin wanda hukumar INEC ta sanyawa Ido.

Sai dai kuma, hukuncin kotun koli ta tabbatar da Lawan a matsayin sahihin dan takara.

Zan zo ka koya mani yadda ka koma majalisa ba tare da takarar zaben fidda gwani ba, Okorocha ga Lawan

Da yake magana a taron kulle zaman majalisar, Okorocha, wanda ba zai koma majalisar ba ya yi mamakin yadda aka yi Lawan ya samu komawa majalisar.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Tsohon Minista Ya Ce Kirista Dan Kudu Ya Dace Ya Gaji Kujerar Lawan, Soki Sauran Masu Nema

Jaridar The Cable ta nakalto Okorocha yana cewa:

"Ban yi takarar kujerar majalisar dattawa ba a wannan karon. Kawai takarar kujerar shugaban kasa na yi. Kai dan siyasa ne mai wayo. Yadda aka yi ka koma majalisar dattawa wani shafi ne a tarihin siyasarmu wanda akwai bukatar mu tattauna shi.
"Na kasance a filin daga tare da kai muna neman shugabancin kasa, ban taba sani yadda ka yi nasarar yin zagon kasa ba, ka bar wasunmu. Nan gaba dole ka koya mun yadda ka aka yi ka aikata haka."

Lawan ya mayarwa Okorocha da martani

A martaninsa, Lawal ya ce:

"Abu ne mai sauki. Na kasance tare da kai a filin daga kuma bayan kayar da mu, mazabata ta ce sun yi tunanin suna bukata na. Sun nemi na dawo kuma tafiya ce mai wahala don sai da muka je kotu.
"Ban ma daukaka karar hukuncin da ya hana ni takara ba. Jam'iyyar da masu ruwa da tsaki ne suka daukaka kara a madadina har zuwa kotun koli, don haka babu wani babban abu. A zahirin gaskiya ba, babu wani abun da za ka koya daga ciki."

Kara karanta wannan

Zabe Saura Kwana 5, Shugaban kasa Ya Gagara Shawo Kan Zababbun ‘Yan Majalisa

Shettima da uwargidar Tinubu sun halarci zaman majalisa

A wani labarin kuma, mun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da matar shugaban ƙasa, Remi Tinubu, sun halarci zaman bankwana na majalisar dattawan Najeriya ta 9.

Channels tv ta ruwaito cewa a yau Asabar, 10 ga watan Yuni, majalisar dattawa ta yi zaman bankwana a zaurenta da ke birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel