An Kara Kashe Bayin Allah a Jihar Arewa Duk da Sa Dokar Kulle, Atiku Ya Maida Martani Mai Zafi

An Kara Kashe Bayin Allah a Jihar Arewa Duk da Sa Dokar Kulle, Atiku Ya Maida Martani Mai Zafi

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da sabbin kashe-kashe da kona gidaje da aka yi a garin Mangu da ke jihar Filato
  • Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar PDP a zaben 2023 ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tashi tsaye wajen yakar rashin tsaro a jihar
  • Ku tuna cewa an sake aiwatar da kashe-kashen mutane a Mangu duk da dokar hana fita na awanni 24 da Gwamna Caleb Mutfwang ya kakabawa garin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam'iyyar PDP a zaben 2023, ya yi alhinin kashe-kashen da ya sake aukuwa a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Kara karanta wannan

Kano: Hukumar Kashe Gobara ta ceto wani matashi da bashin miliyan 2 ya sa zai kashe kansa

Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da kisan Filato
An Sake Kashe Bayin Allah a Jihar Arewa Duk da Dokar Hana Fita, Atiku Ya Yi Martani Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na X, Atiku ya koka kan lamarin sannan ya bayyana shi a matsayin "tashin hankali, inda ake kashe rayukan da ba su ji ba ba su gani ba.

"Ana kona gidaje, da jefa al’umma cikin hargitsi, wannan cin zarafi ne kai tsaye ga zaman lafiya da hadin kai da muke matukar so."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashe-kashe a jihar Filato

Ku tuna cewa gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya sanya dokar kulle na awanni 24 a garin Mangu, amma kuma tashin hankalin ya ki cinyewa inda aka kashe mutane da kona gidaje.

An sanya dokar kullen ne biyo bayan kashe-kashen da aka yi a ranar Talata, 23 ga watan Janairu.

Sai dai kuma, mazauna sun rahoto cewa yan bindiga sun farmaki wasu garuruwa, suna ta harbin mutane da cinnawa gidaje wuta.

Kara karanta wannan

Mai ciki ta haihu a tsaye yayin da ake cigaba da kashe Bayin Allah a Filato

Daga cikin wuraren da aka farmaka harda makarantar Islamiyya ta Sunnah da ke hanyar Gindiri.

Atiku ya magantu kan kashe-kashen Filato

Sai dai kuma, a martaninsa a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu, Atiku ya yi kira ga jami’an tsaro akan su tashi tsaye wajen dakile matsalar tsaro a kasar.

“Ya zama wajibi jami’an tsaron mu su kara azama sosai, musamman idan aka yi la’akari da yadda matsalar ta’addanci ke ci gaba da faruwa a Filato da ma sassan kasar nan daban-daban.
"Rashin sanya ido da daukar matakan kariya daga irin wadannan rikice-rikice abu ne mai matukar damuwa.
Lokaci ya yi da jami'an tsaronmu za su tashi tsaye domin tabbatar da tsaro da walwalar yan kasar."

An sheke yan bindiga da yawa

A wani labarin, mun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga 3 masu garkuwa da mutane sun baƙunci lahira a jihar Adamawa da ke shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa dakarun ƴan sanda ne suka sheƙe su a wani samame da suka kai tare da taimakon mafarauta ƴan sa'kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel