Sallar Gani: Biki mafi girma a Daura

Sallar Gani: Biki mafi girma a Daura

Sallar Gani ya kasance hawan daba da ake gudanarwa a masarautar Daura. A ko wani shekara lokacin bikin Maulidi, wato ranar 12 ga watan Rabiul Awwal a kalandar musulunci, yaya maza da mata na masarautar Daura, dukan dawo gida domin halartan wannan gagarumin biki.

Sallar Gani ya kasance abun tunkawo dake jan hankulan mutane, inda mutane daga sassa daban-daban na duniya kan halarta domin nishadantuwa.

A lokacin bikin, akan yi hawan daba na musamman domin kara kawata taron. Inda a lokutan baya akan shafe kwanaki 10 zuwa 14 domin wannan gagagrumin biki, amma a wannan zamani akan shafe kwanaki biyu zuwa uku ne kawai.

Sallar Gani: Biki mafi girma a Daura
Sallar Gani: Biki mafi girma a Daura

Har ila yau wannan biki yak an zamo matattarar sada zumunta inda mutanen masarautar kan hadu da tsoffin abokai domin a sada zumunci.

KU KARANTA KUMA: Baza’a iya tsige shugaban kasar Najeriya ba a karkashin kundin tsarin mulkin 1999 - Dogara

Hakan ce ta kasance a ranar 3 ga watan Disamban wannan shekarar. An gudanar da hawan daba mai kayatarwa. Kimanin hakimai 16 na masarautar ne suka yi hawa bisa al’adar masarautar. Mazaje sun hau dokuna, maharba na ta harbi, sannan makidan gargajiya da masu rawa na ta nishadantar da jama’a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: