Hedkwatar Tsaro Na Shirin Gayyatan Fitaccen Shugaban Addini Kan Zarginsu da Hannu a Kisan Filato

Hedkwatar Tsaro Na Shirin Gayyatan Fitaccen Shugaban Addini Kan Zarginsu da Hannu a Kisan Filato

  • Hedkwatar tsaro ta ce za ta gayyaci shugaban kunyar CAN a jihar Filato domin tabbatar da zargin da yake yi
  • Rabaran Timothy Daluk, shugaban kungiyar CAN a karamar hukumar Mangu ta jihar, ya yi zargin cewa sojoji na aiwatar da kisan kiristoci da lalata dukiya a yankin
  • A wata sanarwa da ta fitar a safiyar Alhamis, rundunar soji ta nuna cewar bata goyon bayan wani bangare wajen tsaron Filato da Najeriya baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jos, Plateau - Hedkwatar tsaro ta nuna shirinta na gayyatar Rabaran Timothy Daluk, shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan labarai na rundunar, Birgediya Janar Tukur Gusau ya saki.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro na da hannu a kisan kiyashin da ke wakana a Plateau? Gaskiya ta bayyana

Hedkwatar tsaro za ta gayyaci shugaban CAN a Filato
Hedkwatar Tsaro Na Shirin Gayyatan Fitaccen Shugaban Addini Kan Zarginsu da Hannu a Kisan Filato Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa taron da za a yi tsakanin shugaban kungiyar Kiristan da hedkwatar tsaro ya kasance ne sakamakon furucin da Daluk ya yi akan rundunar sojin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku tuna cewa a baya Daluk ya yi zargin cewa rundunar sojin Najeriya na aiwatar da kashe-kashen Kiristoci da lalata dukiyoyi a Filato a kwanaki.

Shugaban CAN ya zargi sojojin Najeriya da son kai a Filato

Malamin addinin ya yi zargin cewa rundunar sojin ta kori dukkan Kiristoci daga sabon kasuwar sannan ta bar Musulmai suna zuwa da kona gidajensu.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, Daluk ya yi wannan zargi ne a cikin wani bidiyo. Ya ce:

"Na zo nan ne don bada rahoton abun da ke aruwa a karamar hukumar Mangu don duniya ta fahimta. Abun da ke faruwa a Mangu a wannan lokaci, rundunar soji sune suke korar mutane don a kona gidajensu."

Kara karanta wannan

Dara za ta ci gida yayin da shugaban EFCC ke fuskantar dauri a gidan kaso kan dalili 1 tak

Rundunar soji ta ce bata nuna son kai wajen tsaron kasar

Martanin hedkwatar tsaro ya kuma bayyana cewa rundunar soji tana shirin gayyatar Daluk ne don ya zo sannan ya tabbatar da ikirarin saboda mutane sun saba sako tausayi a hukuncinsu kan yanayi irin wannan.

An kama gawurtaccen dan bindiga

A wani bidiyon jami'an rundunar tsaro sun yi nasarar kama wani gawurtaccen dan bindiga mai suna Ya'u Babban Kauye da ya addabi al'ummar Zamfara.

Ya'u Babban Kauye ya kasance shugaban yan bindiga wanda ya yi kaurin suna wajen kakabawa al'umman yankin karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara haraji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel