Kano: Dan China Ya Nemi Kotu Ta Masa Sausauci Kan Yi Wa Budurwarsa, Ummita, Kisar Gilla

Kano: Dan China Ya Nemi Kotu Ta Masa Sausauci Kan Yi Wa Budurwarsa, Ummita, Kisar Gilla

  • Frank Geng Quangrong, dan China da ake tuhuma kashe budurwarsa yar Kano, Ummukulsum Sani, ya nemi kotu ta yi masa sassauci
  • Mr Geng Quangrong, ya shaidawa kotun a ranar Talata cewa ba da gangan ya kashe Ummita ba, azabar rike masa maraina da ta yi ne ya ja hakan
  • Mai Shari'a Ado Ma'aji na babbar kotun Kano ya dage zaman shari'ar zuwa ranar 29 ga watan Maris don yanke hukuncin karshe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Dan China, Frank Geng Quangrong, da ake tuhuma da kashe budurwarsa Ummukulsum Sani Buhari, ya musanya kashe ta da gangan, kuma ya roki kotu ta yi masa sassauci.

Kara karanta wannan

Malamin makarantar Islamiyya ya shiga babbar matsala bayan ya lakadawa karamin yaro dukan tsiya

A jawabinsa da ya gabatar gaban babbar kotun da ke Kano a ranar Talata, Quangrong ya yi ikirarin cewa ya daba wa Ummita wuka ne don kare kansa bayan ta rike marainansa a 2022.

Kano: Dan China da ya yi wa Ummita kisar gilla ya nemi kotu ta masa sassauci
Kano: Dan China da ya yi wa Ummita kisar gilla ya nemi kotu ta masa sassauci. Hoto: Dailytrust
Asali: UGC

Mr Geng Quangrong ya roki kotu ta yi masa sassauci

A cewar sa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba da gangan na kashe Ummukulsum ba, na caka mata wuka ne saboda ta rike maraina na."

Ya roki Mai Shari'a Sanusi Ado Ma'aji da ya yi masa sassauci a hukuncin da zai yanke masa.

"Ina rokon wannan kotu mai alfarma ta yi mun sassauci a hukuncin da za ta yanke bisa la'akari da maganar da na yi a baya," a cewar Geng.

Kotu ta sanya ranar da Mr Geng zai san makomarsa

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Quangrong ya kashe budurwarsa Ummukulsum ne a cikin watan Disambar 2022 bayan samun wani sabani.

Kara karanta wannan

Ya ci kudin banki: Kotu ta daure wani dan jihar Bauchi shekara 3 a gidan yari, an samu bayani

Da kotun ta yi zama kan shari'ar a ranar Talata, Mai Shari'a Ado Ma'aji ya saka ranar 29 ga watan Maris, 2024 don yanke hukuncin karshe kan tuhumar kisan kai.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan da mai gabatar da kara da lauyan wanda ake kara suka kammala shigar da hujjoji da rufe bayanai kan shari'ar, rahoton Leadership.

Kotu ta garkame matashin da ya ci kudin banki ya ki biya

A wani labarin, babbar kotun jihar Bauchi, ta iza keyar wani matashi mai suna Yusuf Aminu zuwa gidan gyaran hali biyo bayan kama shi da laifin karbar bashin banki kuma ya ki biya.

An ruwaito cewa Aminu ya je bankin FCMB, ya karbi bashin naira miliyan 1.6 da sunan zai kara jari a sana'arsa, sai dai ya kashe kudin tas, kuma ya ki ya biya bankin bashin kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel