Ya Ci Kudin Banki: Kotu Ta Daure Wani Dan Jihar Bauchi Shekara 3 a Gidan Yari, an Samu Bayani

Ya Ci Kudin Banki: Kotu Ta Daure Wani Dan Jihar Bauchi Shekara 3 a Gidan Yari, an Samu Bayani

  • Wata babbar kotu a jihar Bauchi ta aika da Yusuf Aminu zuwa gidan gyaran hali na tsawon shekara uku bayan karbar bashi daga bankin FCMB
  • Hukumar EFCC ce ta shigar da Aminu kara gaban kotun, inda ta bayyana cewa tun a shekarar 2021 ya karbi kudin kuma ya ki biya
  • An ruwaito cewa Aminu ya karbi bashin naira miliyan 1.6 daga bankin FCMB da nufin bunkasa sana'arsa, amma ya cinye kudin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Bauchi - Wata babbar kotu a jihar Bauchi ta garkame wani matashi, Yusuf Aminu a gidan yarin a shekaru uku saboda aikata rashin gaskiya da karbar kudi ta hanyar yaudara.

Kara karanta wannan

Kisan Ummita: Kotu ta tsayar da ranar da dan China zai san makomarsa

Hukumar EFCC reshen shiyyar Gombe ne suka shigar da Aminu kara gaban kotun Mai Shari'a A.M Sambo bisa tuhumarsa da aikata laifi daya, karbar kudi ta hanyar yin karya.

Kotu ta garkame matashi saboda ya karbi bashin banki a Bauchi.
N1.6m: Kotu ta daure matashi shekara 3 saboda ya karbi bashin banki a Bauchi. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Aminu ya karbi bashi daga FCMB ta hanyar yaudara

EFCC a rahoton karar da ta shigar ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yusuf Aminu (wanda ke da kamfani mai suna Yusuf Aminu General Enterprises), a watan Janairu 2021 a jihar Bauchi, ya karbi bashin naira miliyan 1.6 a wajen bankin FCMB.
"Ya yi wa bankin karyar cewa zai yi amfani da kudin don bunkasa sana'arsa, lamarin da ya saba wa sashe na 320 da hukunci a sashe na 322 a dokar 'Penal code'.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Laraba, lauyan EFCC, Mubarak Tijani ya roki kotun ta yanke wa Aminu hukunci kan laifin da ya aikata, bayan da ya amsa laifinsa.

Kara karanta wannan

Mata da miji sunyi karyar yan bindiga sun sace su domin dangi su musu karo-karon naira miliyan 5

Kotu ta daure Aminu amma da tsarin ya biya tara

Sai dai lauyan wanda ake kara, Adamu Baba ya roki kotun da ta yi wa Aminu sassauci karancewar ya amsa laifinsa kuma ya yi nadamar abin da ya aikata.

Mai Shari'a Sambo ya aika wanda ake tuhumar zuwa gidan gyaran hali na tsawon shekara uku, amma da zabin biyan tarar naira dubu 50.

Aminu ya fara zama a magarkama ne tun bayan da ya karbi bashi daga bankin FCMB da nufin bunkasa sana'arsa. Sai dai ya cinye kudin kuma ya gaza biyan bashin da bankin ke binsa.

Ga abinda hukumar ta wallafa:

Kotu za ta yanke hukunci kan dan China da ya kashe Ummita

A wani labarin, babbar kotu a Kano ta ce za ta yanke hukuncin karshe kan shari'ar da ake yi da wani dan China, Mr Frank Geng, da ake zargin ya kashe budurwarsa Ummukulsum Sani.

Duka lauyoyin wanda ake karar da masu karar sun kammala shigar da

Asali: Legit.ng

Online view pixel